2019: GWARZON GWAMNONIN AREWA: Zulum masu karatu suka zaba

0

Cikin makon da ya kare ne PREMIUM TIMES HAUSA ta fitar da Gasar Zaben Gwarzon Gwamnan Arewa na 2019.

Jaridar ta tantance gwamnoni biyar na Arewa da ta ware ta ce masu karatu su fitar da gwanin su.

Wadanda aka fitar domin fafata gasar da su, sun hada da Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, El-Rufai na Kaduna, Gandujen Kanawa, Zulum na Barno da kuma Yahaya Bello na Kogi.

To, sakamakon da PREMIUM TIMES HAUSA ta tattara, bayan kwana hudu masu katatu na jefa kuri’a, ya nuna Babagana Zulum na Jihar Barno ne Gwarzon Masu Katatun PREMIUM TIMES HAUSA, na 2019.

Na biyu Bello Matawalle na Zamfara. Sai El-Rufai ya zo Na uku, Ganduje na hudu sai Yahaya Bello na biyar.

Abin mamaki, Zulum wanda sabon-shiga ne a mulki, amma har ya kayar da gwamnonin da suke kan zangon su na biyu a wajen masu karatu.

Akalla masu karatu sama da 3000 ne suka fadi ra’ayin su game da wannan tambaya da muka yi cikin gwamnonin da muka zabo a shafukan mu na Facebook, Instagram, Tiwita, da whatsApp. Kashi 63 bisa 100 sun zabi Zulum na jihar Barno da Matawalle na Zamfara.

Bello Matawallen Maradun na Jihar Zamfara shima ya samu yabo daga masu karatu domin shine ya zu na biyu daga masu karatu.

Gwamna Babagana Zulum: Aiki ga mai kare ka

Farkon abin da ya fara yi a hawan sa shi ne tabbatar da cewa ya saisaita tsarin ma’aikatan gwamnatin jihar. Ya hana zuwa a makare, ya hana fashi, kuma ya hana ma’aikacin gwamnati zaman dirshan a ofis. Ko dai ka kama aiki, ko a tilasta ka kama aiki ko kuma ka kama hanyar gida.

Zulum ba ya zullumin bayyana gaskiyar magana yadda ta ke. Ko cikin wannan makon ya yi kira ga sojoji su kwato Karamar Hukumar Kukawa daga hannun Boko Haram.

Sannan kuma ya sha zuwa garuruwan da ake tsoron zuwa ya na kwana a can ko ma shafe kwanaki. Lallai ‘matsoraci ba ya zama gwani’, kamar yadda marigayi Shata ya fadi a cikin ‘Bakandamiya.’

Zulum ya maida hankali wajen kafa Cibiyar Kula da Masu Ciwon Koda da sauran ayyukan da ya sa gaba a cikin kankanin lokaci.

Share.

game da Author