Bincike ya tabbatar da cewa idan har kotun kasar Amurka ta kama shugaban kamfanin sufurin jirage na Air Peace, Allen Onyema da laifin harkallar dala milyan 21 da ta ke tuhumar sa, to zai iya shafe shekaru 105 a kurkuku, idan ya na da tsawoncin rai.
Amma kuma caje-cajen da aka yi wa Shugabar Kula da Harkokin Kudade da tsare-tsare, Ejiroghene Eghagha, bai kai na shugaban Air Peace din ba, wa’adin za ta iya kwashew a kurkuku ba zai kai na ogan ta Onyema ba.
Daga cikin binciken da ake yi musu, tuni Amurka ta kwace asusun ajiyar kudaden Onyema a bankin Amurka da Canada, kwatankwacin naira bilyan biyar.
Da ya ke adadin tsawon daurin da ake yi wa wanda aka kama da harkallar kudade a Amurka kan kai har shekaru 30, to hakan na nufin Onyema zai iya fuskantar daurin shekaru 90 na harkallar kudade.
Sai dai kuma da ya ke daurin duk a lokaci daya zai tafi, to tsawon shekarun da zai iya shafewa a daure ba za su wuce 30 ba kenan .
Yayin da Onyema ya karyata zargin da Amurka ke masa, a nan Najeriya kuma lauyoyin sa sun shigar da kara, sun a neman kotu ta hana duk wani yunkuri da za iya yi nan gaba domin a kama Onyema a mika shi Amurka.
Can a Amurka kuma, tuni tun a ranar 19 Ga Nuwamba, jami’an gabatar da masu laifi a gaban alkali a Amurka sun samo sammace daga kotu, mai nuna cewa duk inda aka ga Onyema shi da Eghagha a cikin Amurka, to a damke su kawai.
Haka nan kuma sun aika da wannan sammace ga jami’an tsaron kasar Canada cewa ko Onyema ko Eghagha, duk wanda ya dira Canada a yi gaggawar kama shi.
Wani mai sharhi kan harkokin kasuwanci mai suna Osahon Ojigbede, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa, “A Najeriya ne kadai mutum zai kudance a dare daya, amma duk yadda aka yi kokarin gano yadda ya samu kudin, sai abin ya faskara.”
A tattaunawar da aka yi da shi, Onyema ya ce abin haushi ne da takaici da ake ta yada ji-ta-ji-tar cewa wai shi yaron Patience Jonathan ne, kuma kudaden ta ne ya ke juyawa.
Ya kara da cewa shi tunda ya ke bai ma taba haduwa da Patience ba.
Onyema ya ce shi a Warri ya tashi, sannan daga baya ya koma Lagos, ba da dadewa ba bayan ya kammala digiri a Jami’ar Ibadan. Ya zama lauya cikin 1989.
A lokacin da ya koma Lagos, cikin 1990, sai ya kafa kamfanin lauyoyi, daga baya kuma ya koma harkar hada-hadar rukunin gidaje.
Ya ce ya fara samun nasibin rayuwa a harkar rukunin gidaje, bayan da ya rika rika saida manyan filaye a Lekki da sauran unguwanni masu tsadar gidaje.
“Zuwa 2008, na rika samun kudin ruwa na kashi 18 bisa 100 daga dukkan kudaden da na ke ajiyewa. Don haka da kudin ruwan da na ke samu daga banki na rika gina rukunin gidaje ina sayarwa.” Haka ya shaida wa City People.
Ya ce a cikin 2008 ya tattauna batun kafa kamfanin jiragen sama na Air Peace, tare da matar sa. Sannan kuma ya shafe shekaru da yawa yana fafutikar samun lasisin kafa kamfanin.
Daga nan sai ya rika bayar da labarin yadda ya rika karbar ramce kudade daga Fedility da Zenith Bank, domin kara habbaka jiragen sa.
Ya kalubalanci wanda duk ke tantama, to ya je Fedility Bank ya yi bincike.
Onyema ya ce a yanzun haka Air Peace na da ma’aikata 3,000, wadanda daga ciki kuwa 2,000 duk mata ne.
Ya kuma bayyana yadda matan da ke aiki a karkashin kamfanin na sa ke da azama da kishin aiki da kuma kaunar ganin Air Peace ya habbaka.
Daga cikin matan da ya yaba, har da Eghagha, wadda Amurka ke tuhumar su tare.