ZABEN KOGI: Yadda ’yan sanda da ’yan jagaliya suka rika satar akwatunan zabe a Lokoja

0

A idon wakilin PREMIUM TIMES ’yan sanda suka rika hada kai da ’yan ta-kifen jagaliyar siyasa, da ke dauke da makamai ana sace akwatina da aka rigaya aka jefa kuri’a, a garin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Duk da cewa ba a yi mamakin ganin faruwar hakan ba, amma dai al’amarin ya faru tun farkon fara zaben, kamar yadda mazauna garin suka cika da mamaki.

An fara tantance masu jefa kuri’a a Lokoja wajen karfe 12 na rana. Daga Mazabar Lokoja Club, bangare ta 16, Mazaba ta 1 wasu matasa da ke dauke da muggan samfuran makamai daban-daban, tare da ‘yan sanda sanye da kaki, suka fara kai farmaki.

Wannan mazaba dai ba ta nisa da Gidan Gwamnatin Jihar Kogi, wato Lugard House.

Da farko dai wasu manyan jami’an tsaro sun je wurin, amma jim kadan bayan tafiyar su, sai ga wasu motoci uku dauke da ‘yan sanda da ‘yan iskan jagaliya dauke da makamai.

Da farko dai suka fara cire igiyar kyallen da aka daura, mai nuni da cewa ba a yadda wani ya ketara cikin wurin ba.

Bayan sun kutsa ciki, sai suka tarwatsa wurin, sannan suka kwashe akwatan zabe, daga nan suka fizgi motocin su, suka yi gaba a sukwane.

Su kan su ‘yan sandan da ke aiki a wurin zaben da sauran jami’an tsaro arcewa suka yi a guje, da suka ga bain ya fi karfi su.

Ba a dai yi harbi ko sau daya ba, amma kuma an saci akwatai, kuma an karairaya teburan aikin zabe.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya da ke sa-ido a wurin, su ma sun bar wajen da suka ga halin da ake ciki.

Wadannan mahara ba su saurara wa da suka dira rumfar zabe ta Crowther Memorial College, Rumfa mai lamba 008. Su na dira suka fara harbe-harbe, ta yadda jami’an tsaro, jami’an zabe da masu jefa kuri’a kowa ya dafe keya ya fice a guje.

Wasu ma ba su tsaya bi ta kofar fita daga cikin makarantar ba, tsallaka Katanga da waya suka yi.

Bayan wannan hari, an ga wadanda ‘yan bindiga sun nufi Gidan Gwamnati kai-tsaye, su na tafiya sun a darzaza harbin bindigogi.

Sun kara bi wata rumfar zaben sun saci akwatai. Kuma wuraren da wakilin mu ya bi daga baya gan su a hargitse.

Sai dai kuma wani jami’in INEC ya ce duk takardun zaben da suka sace, to aikin banza suka yi, domin na’irar tantance yawan masu zabe, ‘card reader’ ta na dauke da yawn wadanda suka jefa kuri’a.

Share.

game da Author