ZABEN KOGI: Jefa kuri’a na neman zama gwada-karfin makamai

0

Shugabannin jam’iyyar PDP na Shiyyar Sanatan Kabba, wato Kogi ta Yamma, sun sha da kyar a ranar Larabar da ta gabata. Wasu rikakkun ’yan takifen siyasa ne suka kai mummunan hari, abin da ya kara dagula matsalar tsaro a jihar, kwanaki biyu kafin ranar zabe.

Daga cikin wadanda aka fatattaka har da Joseph Dada, wanda aka ratattaka wa gidan sa da motocin sa ruwan harsasai ratatattata.

Sauran wadanda aka kai wa harin sun hada da Johnson Abejinrin da kuma wani mai suna Obagbayi, wanda shi ma aka ce babban dan jam’iyyar PDP ne a garin Kabba.

Hotunan da suka rika yawo a shafukan kafofin sadarwa sun nuna yadda aka ratattaka wa gine-gine da motoci harsasai. Kuma an ga yadda aka ragargaza gilasan motoci.

Rahotanni daga Jihar Kogi sun tabbatar da yadda ake ta kai wa jam’iyyun adawa munanan hare-hare.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa tuni wasu shugabannin jam’iyyun adawa sun kwashe iyalan su daga jihar zuwa wasu jihohin.

Irin yadda ake amfani da makamai a Jihar Kogi ya kara tabbatar da irin mummunar barazanar da zaben Gwamnan Jihar Kogi zai fuskanta.

Domin a ranar Talata ‘yan daba dauke da muggan makamai sun kai wa hedikwatar jam’iyyar SDP a Lokoja hari, suka banka ma ta wuta, har gobara ta lashe hedikwatar.
An kuma kekketa takardun bayanai na gudanarwar ofishin tare da ragargaza wasu kayyaki masu daraja.

Kuma a kan idon jami’an tsaro suka rika cin zarafin ‘yar takarar gwamna a karkashin SDP, Natasha Akpoti. An tabbatar da cewa magoya bayan Gwamna Yahaya Bello ne suka yi wannan aika-aika.

Abin takaici ne kwarai ganin cewa an kai wa Natasha harin ci ma ta zarafi a hedikwatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC na Jihar Kogi. Kuma a lokacin an je taro ne har da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu.

Duk da cewa ’yan sanda ba su karyata kai wa Natasha hari da magoya bayan Gwamna Bello suka yi ba, har yau ko mutum daya ba su kama ba.

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar GDPN, Dele Williams ya bayyana wa PREMIUM TIMES a cikin wata tattaunawa da jaridar nan ta yi da shi cewa an sha kai wa kwanba din kamfen din sa hari a kwanakin da ya shafe ya na rangaden yakin neman zaben da ya fito takara, wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Ya ce wasu shugabannin jam’iyyar su ko dai sun fice daga jihar saboda tsoron rasa rayukan su, ko kuma wasun su sun fice da iyalan su daga jihar, saboda tsoron kada a kai wa iyalan na su hari.

“Baya ga cin zarafin mu a lokacin kamfen, har barazanar rasa raina sai da aka yi min.” Inji Williams.

Ya kara da cewa duk da sun kai koke-koken su ga Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan, har yau ko fara ba a kama ba. Ga shi kuma rashin tsaron sai kara muni ya ke yi a daidai lokacin da ranar zaben ke kara gabatowa.

Sai dai kuma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kogi, Jibrin Abu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai kamata a rika ta’allaka rikicin da magoya bayan APC ba, saboda magoya bayan jam’iyyar a cewar sa, masu bin doka da oda ne.

Jiya Laraba ne dai Majalisar Dattawa ta amince a bai wa Jihar Kogi zunzurutun kudi har naira bilyan 10.069, matsayin wasu kudade da ta ke bin gwamnatin tarayya bashi, na ayyukan gina wasu titinan gwamnatin tarayya da ta yi.

Wasu sanatocin sun nuna rashin amincewa da bayar da kudin ga Jihar Kogi, bisa tsoron kada a yi amfani da kudaden wajen cin zaben gwamna da za a yi da tsiya ko da tsinin-tsiya.

Share.

game da Author