Ranar Asabar za a yi ta ta kare a zaben gwamnan Jihar Kogi, jiha mai Kananan Hukumomi 21. Jam’iyyun siyasa 23 ne za su fafata tsakanin su, a zaben ha-maza-ha-ma-mata da zai dauki hankalin kasar nan baki daya.
Gwamna Yahaya Bello na APC, mai shekara 44 a duniya, zai daura banten kokawar kare kambun kujerar sa, to kuma ya sha kaye a hannun daya daga cikin manyan abokan hamayya biyu, wato Musa Wada na Jam’iyyar PDP, ko kuma mace mai kamar maza, Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP.
Bello ya zama gwamna a bagas, bayan mutuwar marigayi Gwamna Abubakar Audu, wanda ya ce zabe a karkashin jam’iyyar APC, a 2015. Audu ya rasu a ranar da aka bayyana cewa ya yi nasarar cin zabe.
Bello ya sha kaye a zaben fidda-gwanin APC cikin 2014. Daga nan ba a sake jin duriyar sa ba, sai da INEC ta bayyana cewa zabe bai kammalu ba, aka yi zaben raba gardama a wasu kananan hukumomi, kuma Audu ya yi nasara.
Rasuwar Audu ta sa INEC ta bai wa Bello kujerar gwamna kai-tsaye, domin shi ne ya zo na biyu a zaben fidda-gwanin APC.
Bello zai ci kwakwa a zaben gobe, matsawar za a yi zube-ban-kwarya, kasancewa ya na shan suka sakamakon tabuka abin kirki da bai yi ba a wannan zangon farko da ya ke kan kammalawa.
Babban dan adawa dai shi ne Musa Wada, kanen tsohon gwamna Idris Wada na jam’iyyar PDP. Sannan kuma suriki ne ga tsohon gwamnan jihar Idris Ibrahim na PDP.
Baya ga karfin da PDP ke da shi bakin gwargwado a jihar, Wada na tinkaho da yawan jama’ar Karamar Hukumar Dekina, wadda ita ce mahaifar sa, kuma karamar hukumar da ta fi sauran kananan hukumomi 20 dimbin yawan masu jefa kuri’a a jihar. Idris dan Kabilar Igala ne.
Ta ukun karfi mace ce mai suna Natasha Akpoti, mai shekaru 40 a duniya. Idan har ta ci zabe, to ita ce mafi karancin shekaru a cikin gwamnoni kenan. ’Yar asalin Karamar Hukumar Okene ce, wato karamar hukumar su daya da gwamna Yahaya Bello kenan.
Natasha dai ruwa-biyu ce. Mahaifiyar ta Baturiyar kasar Rasha ce, shi ya sa ma aka rada ma ta sunan da ya yi daidai da na matan kasar Rasha. Mahaifiyar Natasha ta yi aiki a Ma’aikatar Sarrafa Karafa ta Ajaokuta, a jihar Kogi, inda ta hadu da mahaifin ta ya na aiki, har suka yi aure.
Bayan mutuwar mahaifin ta, sai mahaifiyar Natasha ta kwashi ‘ya’yan ta, har da ita, ta koma kasar Rasha da su. A can ne Natasha ta yi karatun jami’a, daga baya kuma ta dawo Najeriya, bayan mahaifaiyar ta ta mutu a Rasha.
A nan Najeriya, Natasha ta yi suna sosai wajen kafa kungiyoyi da rajin neman ’yanci.
Duk wanda ya ce Natasha ba abin tsoro ba ce, to ya yaudari kan sa. Domin a zaben 2019 ta tsaya takarar Sanata a karkashin SDP, kuma ta zo ta biyu da kuri’u har 48,336. Wannan ya nuna idan har magoya bayan ta suka sake ba ta goyon baya a wannan zaben, to za ta ji wa Gwamna Yahaya Bello babban rauni a yankin sa, tunda daga yanki daya suka fito.
Idan shi kuma Musa Wada ya samu kuri’u a yankin sa, inda Karamar Hukumar sa ta Dekina ta ke, wadda ta fi kowace yawan jama’a masu jefa kuri’a, to za a yi ‘kare-jini-biri jini’ kenan a wannan zabe.