ZABEN KOGI: Ga ni a durkushe ina nemar wa gwamna Bello gafara, ku sake zaben sa – Inji El-Rufai

0

A jiya ne Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, suka roki al’ummar Jihar Kogi cewa su “yafe wa Gwamna Yahaya Bello dukkan ‘zunuban’ haka su albashi na tsawon wata da watanni da ya yi, su sake zaben sa.

Sun ce a yi hakuri duk da rashin tabuka manyan ayyuka da Yahaya Bello bai yi ba, su yi hakuri su sake zaben sa. A wannan karon inji su, za a ga ayyuka tukuru daga Gwamna Bello.

Ranar Asabar Juma’a ne dai za a yi zaben gwamnan jihar Kogi, a daidai lokacin da ake kuka da gwamnan ya hana ma’aikata albashi tsawon watanni da dama kuma ya hana sauran hakkokin da suka wajaba gwamnatin jiha ta bai wa ma’aikata.

Da suke jawabai a gangamin taron rufe kamfen din APC na zaben gwamnan Kogi, jiya Laraba a Lokaja, El-Rufai ya ce “a matsayin Bello na gwamna mafi karancin shekaru a cikin gwamnonin Najeriya, ya na iya yin kuskure”

Cikin wadanda suka halarci gangamin kamfen din har da Aisha Buhari, Dolapo Osinbajo, uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da kuma Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Rokon El-Rufai

“Mutane da yawa na cewa Yahaya Bello yaro ne; kuma ya yi rikici ko ya bata da mutane da yawa. To ni dai ga ni a durkushe, ina rokon ku yafe wa Yahaya Bello idan ya yi muku laifi.”

“Ina rokon duk wani wanda ya san Gwamna Bello ya yi masa laifi, to ya yafe masa. Yaro ne karami; zai iya yin kura-kurai. Idan ka na yaro, ka kan yi kura-kurai, amma kuma ka kan koyi darasi daga kura-kuran da ka tabka.

Daga nan El-Rufai ya ce su tuna tsohon gwamna Abubakar Audu ya kawo ayyukan ci gaba a Jihar Kogi. Don haka kada su zuba wa marigayi Audu kasa a ido, kada kuma su bari PDP ta sake komawa mulkin jihar Kogi.

Sannan kuma ya roki jama’a su zabi Sanata Smart Adeyemi, a zaben sanata da za a yi lokaci daya da na gwamna.

Adeyemi zai tsaya takara ne da Sanata Sanata Dino Melaye.

Ku manta da laifin da gwamna Bello yayi muku Aisha Buhari

Ita ma uwargidan Shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta roki al’ummar jihar su manta kuma su yafe dukkan laifukan da Gwamna Bello ya yi musu.

Ta ce kasa biyan kudaden albashi sa Bello ya yi, al’amarin ya faru ne saboda tsawon lokacin tantance ma’aikata da aka dauka ana gudanarwa.

Zaben dai zai yi zafi sosai, domin masu takarar gwamna sun kai 42, wadanda uku daga cikin su mata ne.

Share.

game da Author