Alkaluman zabe sun nuna cewa dole ne sai sanata Dino ya samu zunzurutun kuri’u sama 14,000 bayan nasara a sauran kananan hukumomi biyu da ba a bayyana su ba tukunna kafin ya iya yin nasara akan Smart na APC.
A sakamakon da aka bayyana zuwa yanzu Adeyemi ya samu kuri’u 52,389 shi kuma Dino ya na da kuri’u 37,856.
A lissafe dai Dino zai bukaci karin kuri’u 14,533 daga kananan hukumomi biyu da suka rage ba a bayyana su ba kafin ya iya gadara da yin nasara a zaben.
A yanzu dai ana sauraron sakamakon kananan hukumomi biyu ne.
Ga sakamakon kanana hukumomi biyar dake mazabar Kogi ta yamma
Kaba Bunnu
APC — 15,037
PDP — 8,974
Kogi Koton Karfe
APC — 14,168
PDP — 9,786
Mopa Muro
APC — 4,874
PDP — 3,704
Ijumu
APC — 11,627
PDP — 7,647
Yagba East
APC — 6,683
PDP — 7,745