ZABEN KOGI DA BAYELSA: ‘An hargitsa dimokradiyya’, tilas Buhari ya farka – CDD

0

Cibiyar Rajin Karewa da Jaddada Dimokradiyya mai suna Centre for Democracy and Development (CDD), ta bayyana ce abin da ya faru a zaben gwamna da aka gudanar a jihohin Bayelsa da Kogi, ya tabbatar da cewa dimokradiyya a Najeriya ta afka rami gaba dubu, ta na fuskantar barazana.

A kan haka ne cibiyar ta yi jan hankali ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye ya samar da shugabancin da ya kamata a matsayin sa na shugaban kasar nan.

Da ya ke magana a Abuja wajen wani taro da menama labarai, bayan kammala zaben Kogi da na Bayelsa, Darakan Cibiyar Idayat Hassan ta ce tushen da aka kafa sabuwar dimokradiyya a Najeriya shekaru 20 da suka gabata, ya fara rawa sosai, ya na alamun gaggabewa.”

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta gudanar da zabukan gwamnan Bayelsa da na Kogi duk a ranar Asabar da ta gabata.

Dukkan zabukan dai APC ce ta lashe su gaba daya. Jama’a da dama da kuma kungiyoyi da masu sa-ido na ta karajin cewa an yi amfani da tashe-tashen hankula wajen hargitsa zabe, satar akwatinan zabe da kuma yi wa masu adawa barazana.

INEC ta bayyana cewa David Lyon na APC ne ya lashe zaben Bayelsa da kuri’u 352,552, shi kuma Duoye Diri na PDP ya samu kuri’u.

A jihar Kogi kuwa Gwamna Yahaya Bello ne ya lashe zaben da kuri’u 406,222, Musa Wada na PDP kuma ya samu 189,704.

Wada da jam’iyyar PDP sun ce ba su amince da zaben ba, kamar yadda wasu kungiyoyi, wato YIAGA har da UN suka yi kiran da a soke zaben.

CDD ta ce wannan zabe da ya gudana an yi abin da ba daidai ba, musamman raunata jama’a, kisa, satar akwati, yi wa jama’a barazana da kuma hana su yin zabe.
Ya kara da cewa an tauye wa jama’a hakkin zaben wanda suke so su zaba.

Ta ce irin yanayin da aka gudanar da zabe a jihohin Bayelsa da Kogi, ba abu ne da ko kusa ya yi kama da yadda dimokradiyya ta ke ba.

Sannan kuma ta nuna matukar takaicin yadda aka sayi kuri’u, abin da ta ce sayen ‘yancin jama’a ne aka yi.

Ta bayar da misalin abubuwan da suka faru a Kananan Hukumomin Lokoja, Kabba-Bunu, Ijumu, Okene, Ajaokuta, Dekina da kuma Olamaboro.

Haka nan da Idayat Hassan ta juya kan zaben Sanata tsakanin Dino Melaye da Smart Adeyemi, CDD ta ce an tabka hauragiya sosai, abin da ta ce ire-iren abubuwan da na iya kawo wa dimokradiyya nakasu sosai.

Share.

game da Author