Babban dan adawa da gwamna mai ci Yahaya Bello Musa Wada, kanen tsohon gwamna Idris Wada na jam’iyyar PDP ya kada kuri’an sa tunda safe.
Baya ga karfin da PDP ke da shi bakin gwargwado a jihar, Wada na tinkaho da yawan jama’ar Karamar Hukumar Dekina, wadda ita ce mahaifar sa, kuma karamar hukumar da ta fi sauran kananan hukumomi 20 dimbin yawan masu jefa kuri’a a jihar. Idris dan Kabilar Igala ne.
Ta ukun karfi mace ce mai suna Natasha Akpoti, mai shekaru 40 a duniya. Idan har ta ci zabe, to ita ce mafi karancin shekaru a cikin gwamnoni kenan. ’Yar asalin Karamar Hukumar Okene ce, wato karamar hukumar su daya da gwamna Yahaya Bello kenan.A mazabar ANKPA 1, rumfar zabe oo3 dake Fadar Ejeh a karamar hukumar Ankpa ne aka dakatar da aiyukkan zabe saboda wasu matasa sun arce da kayan zabe a wannan mazaba.
Sai dai tun bayan kada kuri’anta Natasha ta koka game da yadda ake gudanar da zaben gwamnan jihar.
A mazabar ANKPA 1, rumfar zabe oo3 dake Fadar Ejeh a karamar hukumar Ankpa ne aka dakatar da aiyukkan zabe saboda wasu matasa sun arce da kayan zabe a wannan mazaba.
Sai dai kuma a cafke su duka sannan har wasu sun koma gida abinsu.
Bayan haka kuma an kama wasu na raba kudi wa masu zabe wuraren zabe a Lokoja.
Wani matashi ya sha duka a karamar hukumar Okene, da ake zaton mari daya aka yi masa ya rika doka kansa a bango, ko ina yayi kulu-kulu sai da aka kamo shi.