ZABEN BAYELSA: APC ta lashe rumfunar zaben dake yankin mazabar Jonathan kakaf

0

Jam’iyyar APC ce ta lashe zaben mazabun da aka riga aka kirga a karamar hukumar Ogbia dake jihar Bayelsa.

Karamar hukumar Ogbia ce mahaifar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sai dai kash sakamakon zaben da aka riga aka bayyana a Yenogoa, dukka APC ce ta lashe zabukan rufunar zaben kaf da kuri’u masu yawan gaske.

Idan ba a manta ba, Jonathan ya dade yana takun saka a tsakanin sa da gwamnan jihar, Seriake Dickson kan dan takarar da PDP za ta tsaida.

Duk da kokari da yayi domin ganin zabin sa ne ya zama dan takara, gwamnan Dickson ya ki amincewa.

Ga sauran sakamakon zaben

Ward 4

APC – 3,683
PDP – 482

Ward 7 (Emeyal) Ogbia LGA

APC – 2,175
PDP – 1,175

Ward 6

APC – 7,883
PDP – 670.

Ward 12

APC – 2,804
PDP – 1,589

Ward 2, Ogbia LGA

APC – 8,716
PDP – 1,850

Share.

game da Author