Mazauna Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa sun tashi da safiyar yau Asabar suka rika ganin dandazon jami’an tsaso ko ina a dukkan manyan mahadar titinan birnin, a daidai lokacin da za su fata fita jefa kuri’ar wanda su ke so ya zama gwamnan su.
Wakilin mu ya zagaya cikin Yenagoa da safiyar yau, ya ga jami’an tsaron da aka jibge a mahadar titinan Imgbi, Opolo, Akenfa, Igbogene, Okarki da kuma mahadar Gateway.
Sannan kuma ya ga an jibge jami’an tsaro a Babban Randabawul na Tombia, wurin da za a iya cewa nan ne tashar yin lodi da saukewa na motoci masu yawa a Yenagoa.
Duk da cewa an jibga jami’an tsaron, wakilin mu da safiyar nan bai ga su na hana jama’a wucewa a kan titinan ba.
Wasu mazauna birnin sun bayyana cewa ganin jami’an tsaro ko’ina ya sa jama’a da daman a fatan cewa za a yi zabe ba tare da tashin hankali ba.
“Ni dai ban ga ‘yan sanda na cin zarafin ko mutum daya ba. Kawai dai motoci su ke bincike, wadanda ba na aikin zabe ba. Hakan kuma ya na da kyau.” Ta bakin Henry Onari kenan, wani ma’aikacin gwamnatin jihar.
Da yawan mutanen da aka yi hira da su sun bayyana cewa dama yau ranar zabe ce, don haka ba za a yi tsammanin ganin karakainar motoci haka kawai a kan tiri babu dalili ba.
Sun ce don haka binciken motocin da ba na daukar kayan zabe, ko jami’an zabe ba, ai ba wani abu ba ne, shi ya sa ba su korfafin ganin yawan jami’an tsaron.