Abdul’aziz Musa Yar’Adua, wanda kani ne ga marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’Adua, ya jinjina wa al’ummar Jihar Bayelsa saboda tunanin zaben David Lyon, dan takarar jam’iyyar APC da suka yi.
Abdul’aziz yayi wannan godiyar ce a cikin wani sakon bayani da ya fitar jiya Litinin a Kaduna.
Tsohon Kanar din mai ritaya, ya kuma gode wa al’ummar jihar Bayelsa saboda sun guje wa aikata dabanci da ta’addanci a lokacin zabe, wanda ya kira cewa sun zabi wanda ya cancanta.
Yar’Adua, wanda har ila yau shi ne kuma Kodinata na Kasa na APCAF, wato manyan ‘yan APC masu neman sauyi, ya yi roko ga sabon zababben gwamnan da ya jure ya aikata ayyukan raya jiya da inganta rayuwar jama’a a Bayelsa.
Daga nan kuma ya yaba wa magoya bayan APC da sauran ‘yan Najeriya kasancewa sun fita sun jefa kuri’un su a cikin kwanciyar hankali.
Ya kuma yi roko ga wadanda ba su samu nasara ba su hakura, su hada hannu domin a sake gina jihar Bayelsa.
Sannan ya jinjina wa Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva, saboda zage damtsen da ya yi ba dar ba rana wajen jan hankalin al’ummar jihar Bayelsa, ya kai su ga nasarar zaben gwamna a karkashin APC.
“Ina kuma kara yin godiya ta musamman ga Gwamnonin Jihohin Jigawa, Kebbi saboda tsayawar da suka yi tsayin daka gaba daya lokacin zaben jihar Bayelsa.”