‘YAR-KURE: Dan Majalisar Tarayya ya kalubalanci Fashola su karade titinan kasar nan tsawon kwanaki 90

0

Karin maganar nan da Hausawa ke cewa, ‘baki shi ke yanka wuya’, a yau ta tabbata a kan Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, wanda ya yi ikirarin cewa titinan kasar nan ba su yi lalacewar da ake ya yamadidi a Najeriya ba.

A kan haka ne Dan Majalisar Tarayya, Bamidele Salam na PDP, ya kalubalanci Fashola cewa ya zo zai dauki nauyin sa da nauyin ‘yan jaridu da masu daukar hotuna, su karade titinan kasar nan domin shi ministan ya gani da idon sa yadda suka lalace.

Salam dai ya na wakiltar Kananan Hukumomin Ede ta Arewa, Egbedore ta Kudu da kuma Ejigbo.

Fashola ya yi wannan bayani jiya bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Kasa, inda ya shaida wa manema labarai cewa, ‘na san wannan bayanin nawa shi ne zai zama labarin da zai karade kasar nan, amma dai ni na san titnan Najeriya ba su yi lalacewar da ake ta kururutawa ba.”

Kalubale

Yayin da Salam ke maida wa Minista Fashola raddi a gaban ‘yan jarida ranar Alhamis, ya bayyana cewa, “Ina ganin cewa jin yadda Ministan Ayyuka Fashola ya nanata wannan ikirari na sa har sau biyu a wurare daban-daban, ya nuna yadda ma’aikatan wannan gwamnati ba su ma san halin da al’ummar su ke ciki ba.

Ya ce manyan jam’ian gwamnati ba za su taba sanin mummunan halin da titinan fadin kasar nan ke ciki ba, har sai sun zama sun rika hawan tittinan su na zirga-zirga kamar yadda talakawa ke yi tukunna.

“A matsayi na na daya daga cikin mamba na kwamitin duba ayyukan titinan kasar nan, ina kalubalantar Fashola ya shirya ya zo mu yi rangadin karade titinan kasar nan tsawon kwanaki 90.

“Shi da duk wani wanda hakkin kula da titinan kasar nan ya rataya a wuyan su, su fito mu yi yawo a kan titinan kasar nan, kada su sake hawa jirgin sama har tsawon kwanaki 90. Za su gane wa idon su irin yadda titinan kasar nan suka lalace.

Fashola ya sha caccaka daga dimbin ‘yan Najeriya a shafukan zumunta na twitter da sauran su.

Bamidele ya kalubalanci Fashola cewa a tafi rangadin tarfe da ‘yan jaridu da masu daukar hotuna, kuma shi zai dauki nauyin komai daga aljihun sa.

Wadanda suka rika caccakar Fashola sun rika watsa masa ruwann zafin bakaken kalamai, tare da kawo masa hujjoji da hotunan titinan garuruwa ko jihohin da suka lalace.

An rika muzanta Fashola cewa tun daga lokacin da ya shiga gwamnati ya daina adawa, ya manta da irin alkawarin da suka rika yi wa dimbin jama’a, wadanda a yanzu a tsirara ake kallon su Fashola. Wasu ma sun rika kiran sa mayaudara.

Da yawa sun rika cewa ya manta lokacin da ya ke adawa, kuma da adawa yake yi har yanzu, ba zai furta wannan kalami na cin zarafi ga ‘yan Najeriya ba.

An kuma rika yi masa gorin cewa a yanzu duniya ta samu, ya shiga mulki, ba ya yawo, iyakar sa Lagos zuwa Abuja kawai, kuma a kan jirgin sama ya ke tafiya, babu ruwan sa da shiga mota daga wannan gari zuwa wancan, don haka bai san halin da titinan kasar nan, jama’ar da ke bi kan titin da irin hadurran da ake yi a kan titin ba.

Sun nuna cewa bai ma san irin asarar rayukan da ake a kullum a kan titinan kasar nan ba, sakamakon rashin kyau da lalacewar titina.

Share.

game da Author