’Yan kasuwan kasar Ghana sun fara kulle shagunan ‘yan Najeriya

0

Ranar Talata an wayi gari ‘yan tireda a Dandalin Opera Square da ke Accra, babban birnin kasar Ghana, suka rika kulle kantina mallakar baki ‘yan kasashen waje.

Sai dai kuma rahotanni sun tabbatar da cewa akasarin kantinan da aka kulle din duk na ‘yan Najeriya ne.

Wannan ne karo na uku da ‘yan asalin kasar Ghana suka kulle kantinan baki daga kasashen waje mazuna kasar.
Kullewar baya-bayan nan kafin ta jiya Litinin, an yi ta ne a cikin watan Yuli na wannan shekarar.

Ba a dai san dalilin kulle wa baki shagunan su ba, wanda wannan ne karo na uku da hakan ke faruwa.

Shi kuwa Shugaban Kungiyar ‘Yan Najeriya Masu Kasuwanci a Ghana, Chukwumeka Nnaji, ya shaida cewa tabbas an kulle kantinan, amma har zuwa lokacin da ake tattaunawa da shi, bai kai ga tantance adadin yawan kantinan da aka kulle ba.

“Watakila za su iya haura 50, ko kuma kasa da haka, kamar dai yadda na ji labari. Amma ban kai ga tabbatar wa ba tukunna.

Wata kafar yada labarai mai suna Citinewsroom, ta tabbatar da cewa ya zuwa 12 na ranar jiyar Litinin an kulle kantina sama da 50, kuma akasari duk na ‘yan Najeriya.

‘Yan tiredar Ghana su na korafin cewa irin tsarin kasuwancin da bakin ke yi ya saba wa Sashe na 27 na Doka da Ka’idojin Cibiyar Bunkasa Kasuwanci ta Ghana, GIPC.

DOKOKIN HANA ‘YAN KASASHEN WAJE KASUWANCI A GHANA

Dokar farko ta haramta wa ‘yan kashen waje gudanar da saye da sayarwa a cikin kananan shaguna ko kasa kaya a kan tebur ko yawon talla a ko’ina.

An haramta wa ‘yan kasar waje gudanar da tuka taxi a karkashin kamfanin zirga-zirgar da motocin da ke karkashin sa ba su kai 25 abin da ya yi sama ba.

Doka ta uku an haramta wa ‘yan kasar waje yi ko bude wurin yin kitso, karin gashi ko aski.

Doka ta hudu kuma an haramata wa ‘yan kasashen waje mazauna Ghana harkar buga katin waya su na sayarwa.

An kuma hana su buga litattafai da makamantan harkokin dab’i.

An hana su bude gidan sarrafa ruwan leda, wato ‘pure water’, kuma an haramta musu sayar da shi.

An kuma haramta wa baki ‘yan wata kasa ba ‘yan Ghana ba sayar da magunguna da bude shagunan sayar da magunguna (chemists).

An haramta musu gudanar da duk wani nau’i na cacar ‘lottery’, sai ta kwallon kafa kadai.

Wani dan dan tireda da aka zanta da shi, ya bayyana cewa: “Idan har ‘yan sanda ba za su iya hana baki ‘yan kasashen waje gudanar da sana’o’in da aka haramta musu ba, to mu za mu iya hana su. Shekara da shekaru sun a shiga gonar mu. To daga yanzu ba za mu kara hakura ko dangana ba.”

An kulle kantinan baki yawanci ‘yan Najeriya a birnin Accra, kwanaki hudu bayan an yi irin haka a birnin Kumasi da ke gundumar yankin Ashanti.

Share.

game da Author