An bindige wasu ‘yan sanda uku har lahira daga cikin wadanda ke aiki a Ofishin ‘Yan Sanda na Fadan Karshi da Sabon Gida, a cikin Karamar Hukumar Sanga cikin Jihar Kaduna.
Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Abubakar Abba ya tabbatar wa manema labarai afkuwar wannan lamari a yau Laraba.
Ya kara da cewa an kwashi gawarwakin jami’an tsaron uku an kai su Babban Asibitin Gwantu.
“’Yan sanda biyu dai a nan take suka mutu, dayan kuma ya mutu a kan hanya kafin a karasa asibiti.”
Sannan kuma jami’an sun ce sun shiga binciken neman wadanda suka yi wannan aika-aika. Sun kuma roki jama’a su kwantar da hankalin su.
Ya nuna damuwar sa dangane da yawaitar aikata manyan laifuka a yankin, tare da kara yin kira ga jami’an tsaron da ke yanke su kara zage damtse.
Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan sandan Kaduna, Suleiman Abubakar, ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.
Suleiman ya kara da cewa za su sanar da abin da ake ciki ba da dadewa ba.
Duk da kokarin da jami’an tsaro ke tutiyar su na yi wajen dakile manyan laifuka, ana ci gaba da samun kisan jama’a da garkuwa da mutane da yawan fashi da makami, musamman a kudancin Kaduna da kuma hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Akasarin matafiya yanzu sun gwammace su hau jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, ko kuma daga Kaduna zuwa Abuja.