Yahaya Bello ya lashe zaben Kogi

0

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi. Bello ya kada abokin takarar sa Musa Wada na jam’iyyar PDP da ratar kuri’u sama da 200,000.

Malamin zabe Ibrahim Garba, da ya bayyana sakamakon a Lokoja ya bayyana cewa kuri’un da aka bata su ba su kai yawan ratar kuri’un da Bello ya kada Musa na PDP da shi ba.

Yahaya Bello na APC ya samu kuri’u 406,222, Musa Wada na PDP kuma kuri’u 189,704. Sannan an lalalta kuri’u 149,576.

Natasha Akpoti ta jam’iyyar SDP ce ta zo na uku da kuri’u 9,482 Kacal.

Bello ya yayi nasara a kananan hukumomi 12 cikin 21 dake jihar da suka hada da Lokoja, Ibaji, Adavi, Okehi, Okene, Kabba Bunu, Ogori Magongo, Koton Karfe , Mopa Muro, Ajaokuta, da Olamaboro.

Musa Wada na PDP yayi nasara a kananan hukumomin Omala , Igalamela , Yagba East, Yagba West, Idah, Dekina , Bassa, Ofu, da Ankpa.

Sai dai tuni har jam’iyyar PDP ta yi watsi da wannan sakamako cewa bata amince da shi ba.

Ana ta bangaren kuwa APC ta yaba wa hukumar zabe ne bisa yadda aka gudanar da zaben.

Share.

game da Author