Yadda Najeriya zata amfana da Kungiyar ‘Mayu’

0

Cibiyar B.I.C Ijomah dake gudanar da bincike kan hanyoyin samar da ci gaba na jami’ar Najeriya dake Nsukka jihar Enugu ce ta shirya taron kungiyar Mayu a wannan makon.

Shugaban cibiyar farfesa Egodi Uchendu wacce ta kware a karatun tarihi da harkokin kasashen waje ne ta jagoranci taron.

Uchendu ta lissafa wasu hanyoyi da idan ama yi amfani dasu da ga cikin shawarwarin da kungiyar ‘Mayun suka bada za a samu ci gaba a Najeriya.

1. Uchendu ta ce cibiyar ta shirya wannan taro ne domin gudanar da bincike kan menene tsafi da maita, yadda maita ke canjawa sannan da yadda wannan canji zai kawo ci gaba.

2. Muna kuma so mu gano ko wani dalili ne ya sa mutane suke gudun shiga kungiyan ‘Mayu’ sannan kuma wadanda suje ciki me suke amfana da.

3. Za a kuma gano ko wani irin gudunmuwa ne wannan kungiya ta ‘Mayu zai bayar wajen ci gaban jama’an kasa, Jami’an tsaro, jami’an tsari, ‘Yan siyasa da dalibai a makarantu.

4. A dalilin wannan taro muna so mu kara bayyana wa mutane wasu abubuwan da basu sani ba game da wannan kungiya da kuma irin amfanin da ta ke da shi. Sannan kuma zamu duba dokokin kungiyar da yadda ‘Mayu’ za su rika gudanar da ayyukan su.

Idan ba a manta ba a ranar Talata ne aka fara wannan taro wanda aka kammala shi ranar Laraba.

Kafin a bari su shirya wannan taro na Ibada, kungiyoyin kiristoci na jihar Enugu musamman mabiya darikar Katolika sun rika yin suka akai suna yin tir da wannan kungiya sannan kuma da neman a hana su yin wannan taro.

PREMIUM TIMES ta tattauna da wani dan jarida da ya halarci taron mai suna Patrick Egwu.

A hira da aka yi da shi wannan dan Jarida ya ce tabbas ya halarci wannan taro ne domin ya gani wa kansa tabbacin ko da gaske ne akwai irin wannan kungiya sannan kuma har ta na da mabiya kamar yadda ake tallatawa?

Ya ce bayan mabiya sun halarta sai aka fara addu’o’i sannan da amshi daga mabiya. Mawaka ma sun rera wakoki na yabo kafin nan aka fara jawabai.

Egwu yace babbancin da ya gani shine a wajen jawabin manyan baki.

“Duk mai jawabin da ya yi magana a taron ya gabatar da jawabinsa ne akan Tsafi da Maita.

Ya ce tun da aka fara taron babu tashin hankali da aka samu daga bangaren mutanen da suke adawa da taron. Sannan daga wajen harbar dakin taron an rika siyar da takardu da kasidu da ke kunshe da yadda ayyukan maita da tsafi suke domin mabiya su rika karantawa.

” Duk da suka da aka rika yi wa wannan kungiya da taro, kafin kace wani abu, mutane sun cika fam a wannan dakin taro. Babban dalilin da ya sa aka shirya wannan taro kamar yadda na gani shine domin a wayar wa mutane kai game da wannan kungiya ta Mayu da rashin illar ta.

Bayan haka Mr Egwu ya ci gaba da cewa ba tun yanzu ba yake ta son sanin ko menene ya hada maita da addinin kirista domin sau da dama zaka ga mutumin da ke ikirarin wai shi kirista ne ya tashi cikin dare ya kunna wuta ya na rokon wai Allah ya kashe makiyinsa. Duk ire-iren haka ai ba daidai bane shima idan aka bi diddigi ayyukan maita ne.

” Abu daya da nake ganin ba a yi daidai ba wajen kushe wannan kungiya shine yadda ake nuna musu kiyayya. A kasashen Turai sai kaga ana ire-iren wadannan abubuwa amma muna tsalle muna yaba musu muna jin dadi wai suna burge mu amma namu sai kaga ana binshi da muggan kalamai da suka.”

Share.

game da Author