Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kudaden da za ta rika saki domin gudanar da manyan ayyuka a kasafin 2020, za su fi bayar da karfi ne wajen gyara titinan da suka lalace.
Ministar Harkokin Kudade da Tsare-tsare ce, Zainab Ahmed ta bayyana haka a yau Laraba bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.
Ta bayyana wa manema labarai cewa, “duk da dai ba za a iya bada garantin samun kashi 100 bisa 100, amma duk kudaden da za a sake domin gudanar da manyan ayyukan raya kasa, to Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje sun a a sahun gaba tare da Ma’aikatar Sufuri ta Kasa.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasafin naira bilyan 267 ga Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje a kasafin 2020. Mafi yawan ayyukan kamar yadda Minista Zainab ta bayyana, za a fi bada karfin yin su ne wajen ginawa da gyaran titinan da suka lalace.

“Abin ne sai a hankali. Kudaden da ake kashewa na ayyukan yau da kullum sun yi tsauri sosai. Haka kuma ba a samun kudaden haraji kamar yadda ake tsammani. Amma dai lokaci zuwa lokaci idan kudi suka shigo, to abin maida hankali shi ne ma’aikatun makamashi, zirga-zirgar sufuri da kuma ta ayyuka da gidaje.”
Daga nan sai Minista ta kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta shigo da tsarin yadda kamfanonin ‘yan kasuwa za su rika yin hadin guiwa su na gina titina, Musamman.
A yanzu haka ta ce akwai kamfanoni masu zaman kan su har 19 da ke aikin ginawa da gyaran titina a fadin kasar nan.
Sannan kuma ta yi magana a kan tasirin da tsarin kudin Sukuk ya y i wajen gyara titinan kasar nan.
Minista Zainab ta yi wannan jawabi makonni biyu bayan da Minsitan Ayyuka daGidaje, Tunde Fashola ya yi kasassabar cewa, titinan Najeriya ba su yi lalacewar da ake ta zugugutawa ba.