Lokacin da labari ya bazu a makon jiya cewa kasar Amurka ta ce Allen Onyema ya yi harkallar milyoyin dalolin da ya shigar da su Amurka, tambayar da jama’a suka rika yi a nan Najeriya, ita ce, yadda Onyema ya samu kudi, ya kafa kamfanin sufurin jirage na AIR PEACE. Saboda a baya, an san ba shi da ko alamar wadannan kudade.
Amma abin mamaki, sai ga shi a cikin shekaru biyar Onyema ya kafa kamfanin jiragen da ya yi karfi, har ya na gwada kafafu da kafada da manyan kamfanonin sufurin jirage.
Wadansu masu sharhi ma cewa suka rika yi, buga masa tambarin cewa dan harkalla ne da Amurka ta yi, ya kara tabbatar da zargin da suke yi masa cewa tantirin dan damfara ne, kamar sauran manyan ‘yan damfarar da kan yi kudi a dare daya a Najeriya.
Wasu kuma zargin da suke yi masa shi ne, kudaden ba na sa ba ne, shi kawai ejan ne na wasu gaggan ‘yan siyasar da suka saci makudan kudaden Najeriya, suka kimshe su a hannun sa.
Onyema dai ya kafa Air Peace Limited cikin 2013, kuma zuwa karshen 2018, kamfanin ne ke da jari mafi karfi a Hukumar Kula da Aikin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA).
Gagara Gasar Kamfanonin Jiragen Najeriya
Air Peace ya samu nasibi da karbuwa a kasashen waje wajen zirga-zirga, domin kakaf a jiragen sufuri na Najeriya, babu wanda ya kai Air Peace yin zirga-zairga a Nahiyar Asiya, Turai da sauran kasashen Afrika.
Tun da farkon wannan shekara, sai da kamfanin ya bayyana cewa zai fadada garuruwa da kasashen da ya ke zirga-zirga, wadanda za su hada da biranen Atlanta da Houston na Amurka.
Onyema: Biri Ya Yi Kama Da Mutum
Zargin da kasar Amurka ta dankara a kan Onyema, ranar Juma’ar da ta gabata, ya rasa sa dimbin jama’a sun kara yarda da cewa mai kamfanin Air Peace rikakken dan harkalla ne.
Ma’aikatar Shari’a ta Amurka dai ta ce ana tuhumar Onyema a kotu da laifin harkalla, damfara, wuru-wuru, sata da jigilar kudade ba kan ka’idar Amurka ba.
Daga sauran wadanda ake tuhuma tare da Onyema, har da wata mata, wadda ita ce Shugabar Hada-hadar Kudade da Tsare-tsare ta Kamfanin Air Peace, mai suna Ejiroghene Eghagha.
Onyema: Mai Tsoron Aradu Shi Ta Ke Kashewa
A tuhumar da ake yi masa, an bayyana yadda shi da Enghagha suka rubuta cakin fitar da kudaden sayen jirage a Amurka har sau biyu, Wato bayan an fitar da kudaden sayen jiragen, sai kuma aka sake fitar da wasu kudaden, da nufin sayen jiragen, bayan an rigaya an biya kudin su.
Well Fargo ya biya wadannan kudaden ne a ranar 10 Ga Fabrairu, 2017 da kuma ranar 20 Ga Fabrairu, 2017.
A kan dalilin wadannan cakin kudade ne shi kuma shi kuma mashahurin bankin nan na Amurka, Well Fargo ya tura tsabar kudi har dala milyan 21 a cikin asusun kamfanin harkar jiragen sama na Springfielf Aviation mallakar Onyema da ke Amurka.
Cikin sa’o’i kadan bayan fitar wannan labari, Onyema ya bayyana cewa bai yi wani laifin wata harkallar da har Amurka za ta maka shi kotu ba. Ya kara da cewa zai kare martabar sa kotu.
Amma dai bai bayyana cewa zai garzaya Amurka domin yak are kan sa a kotu ba tukunna.
Onyema: Kurin Yaro Na Gida Ne
A halin da ake ciki dai yanzu jami’an gabatar da masu laifi a gaban alkali a Amurka sun samo sammace daga kotu, mai nuna cewa duk inda aka ga Onyema shi da Eghagha a cikin Amurka, to a damke su kawai.
Haka nan kuma sun aika da wannan sammace ga jami’an tsaron kasar Canada cewa ko Onyema ko Eghagha, duk wanda ya dira Canada a yi gaggawar kama shi.
Wani mai sharhi kan harkokin kasuwanci mai suna Osahon Ojigbede, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa, “A Najeriya ne kadai mutum zai kudance a dare daya, amma duk yadda aka yi kokarin gano yadda ya samu kudin, sai abin ya faskara.”
A tattaunawar da aka yi da shi, Onyema ya ce abin haushi ne da takaici da ake ta yada ji-ta-ji-tar cewa wai shi yaron Patience Jonathan ne, kuma kudaden ta ne ya ke juyawa.
Ya kara da cewa shi tunda ya ke bai ma taba haduwa da Patience ba.
Onyema ya ce shi a Warri ya tashi, sannan daga baya ya koma Lagos, ba da dadewa ba bayan ya kammala digiri a Jami’ar Ibadan. Ya zama lauya cikin 1989.
A lokacin da ya koma Lagos, cikin 1990, sai ya kafa kamfanin lauyoyi, daga baya kuma ya koma harkar hada-hadar rukunin gidaje.
Ya ce ya fara samun nasibin rayuwa a harkar rukunin gidaje, bayan da ya rika rika saida manyan filaye a Lekki da sauran unguwanni masu tsadar gidaje.
“Zuwa 2008, na rika samun kudin ruwa na kashi 18 bisa 100 daga dukkan kudaden da na ke ajiyewa. Don haka da kudin ruwan da na ke samu daga banki na rika gina rukunin gidaje ina sayarwa.” Haka ya shaida wa City People.
Ya ce a cikin 2008 ya tattauna batun kafa kamfanin jiragen sama na Air Peace, tare da matar sa. Sannan kuma ya shafe shekaru da yawa yana fafutikar samun lasisin kafa kamfanin.
Daga nan sai ya rika bayar da labarin yadda ya rika karbar ramce kudade daga Fedility da Zenith Bank, domin kara habbaka jiragen sa.
Ya kalubalanci wanda duk ke tantama, to ya je Fedility Bank ya yi bincike.
Onyema ya ce a yanzun haka Air Peace na da ma’aikata 3,000, wadanda daga ciki kuwa 2,000 duk mata ne.
Ya kuma bayyana yadda matan da ke aiki a karkashin kamfanin na sa ke da azama da kishin aiki da kuma kaunar ganin Air Peace ya habbaka.
Daga cikin matan da ya yaba, har da Eghagha, wadda Amurka ke tuhumar su tare.
Discussion about this post