Tilas sai manoman Afrika sun mike tsaye sun karfi sauyi noman zamani ka’in-da-na’in idan su na so harkar noma ta zama hanyar samar musu makudan bilyoyin kudade a wannan nahiya nan da shekarar 2030.
Wannan bayani shi ne bayanin bayan taron da wani kwamiti ya gabatar bayan kammala taron Inganta Tattalin Arzikin Afrika da aka gudanar a ranar Talata a Abuja.
Masana harkokin tattalin arziki daga kasashen Afrika daban-daban ne suka halarci taron.
Taro ne da ya kunshi masana harkokin tattalin arziki daga bangaren gwamnati, masu zaman kan su, ‘yan kasuwa kamfanoni, manyan masana daga jami’o’i da kungiyoyin sa-ido kan tattalin arziki. Sukan zauna su tattauna mafita da kuma hanyar inganta tattalin arziki da habbakar sa a nahiyar Afrika.
Wannan taro da aka gudanar tsawon kwanaki uku, ya maida hankali ne kacokan a kan hanyoyin hanyoyin magance kalubalen da masana’antu ke fuskanta.
Domin kokarin neman cimma kudirin wannan sauyi, masanan sun bayyana cewa Afrika na matukar bukatar a dauki harkar noma matsayin harka ce ta samun makudan kudade.
Bincike ya nuna cewa Afrika na da akalla kananan manoma milyan 33 wadanda ba su da tagomashin samun ingantacciyar kasuwar kayan noma da kuma rashin kayan noma na zamani.
Wadannan kalubale ya na kashe musu kwarin-guiwa kuma ya na rage musu ribar da ya kamata su rika samu mai yawa a harkokin noma.
Binciken ya kara nuni da cewa amma idan aka kara habbaka wannan fanni, to za kara samun har milyoyin ayyukan yi a fannin noman zamani mai kawo makudan riba da kudaden shiga.
Da ya ke jawabi a wurin taron, Darakatan MECA masu samar da injinan kayan noma na zamani, Ishaku Gashinbaki, ya bayyana cewa injinan noma na zamani na da muhimmiyar rawar takara wajen inganta noma a Afrika.
“Sai dai kuma abin takaici ba a bai wa wannan bangare na amfani da injina domin kawo sauyi da inganta harkokin noma a Afrika.
Ya ce binciken da MECA ta gudanar a fannin amfani da noman zamani, ya nuna cewa a Najeriya sun gano taraktoci 131,000 sun lalace, yayin da 55,000 kuma na bukatar gyara.
Domin sake gyara taraktocin da suka lalace, ana bukatar akalla naira tiriliyan daya.
Masana da mahalarta da dama sun yi jawabai daban-daban a wurin taron wanda aka shafe kwanaki uku ana gudanarwa.