Yadda Isa Funtua da wasu makusantar Buhari suka ziyarci Sowore a boye don ayi sulhu

0

A wani salon ayi sulhu tsakanin gwamnati da fitaccen dan jarida, mawallafin jarida Sahara Reporters, kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Yele Sowore, wasu ‘yan sakon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun ziyarce dan jaridan a asirce domin a shawo kan rikicin da ya turnike Sowore da gwamnati da ya kai ga har an tsare shi a hukumar SSS.

Idan ba a manta ba hukumar tsaro ta SSS ta tsare Sowore a bisa dalilin zargi da ake masa na shirya zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari.

An yi ta kai ruwa rana a tsakanin lauyoyin sa da na gwamnati inda a karshe dai kotu ta ba da belin sa.

Sai dai kuma duk da beli da kotu ta bada, hukumar SSS din bata sake shi ba.

PREMIUM TIMES ta gano cewa har sau biyu wasu daga cikin makusantar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun garzaya inda ake tsare da Sowore domin tattaunawa da shi don ya hakura da wannan kira da yake yi na ayi wa gwamnati bore har sai an samu gyara da canji kasa.

A tattaunawar wanda Sam Amuka, mawallafin jaridar Vanguard; Nduka Ogbaigbena, mawallafin jaridar Thisday, kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu da mai ba shugaba Buhari shawara kan Harkokin Yada Labarai Femi Adeshina suka halarta, Sowore ya kafe a kan bakarsa, cewa ko an sake shi, ba zai hakura ba zai ci gaba da abinda ya sa a gaba ne nema ya ‘yan Najeriya mafita daga matsatsin da ake ciki.

Hakan nuni ne cewa lallai shugaba Buhari ya san da abin da hukumar SSS ke yi da kuma cewa tsare Sowore shine matsayar gwamnati.

Sai dai kuma mawallafin Jaridar Thisday ya musanta cewa da shi aka ziyarci Sowore a inda yake tsare. Ya ba shi a cikin ‘yan sakon.

Da muka nemi sanin tabbacin wannan ziyara daga bakin wani babban makusancin shugaba Buhari, Sama’ila Isa Funtua, ya shaida mana cewa tare da mawallafin jaridar Thisday suka ziyarci Sowore a inda yake tsare, ba kamar yadda ya abi Obaigbena ya shaida mana ba.

Ya ce sun ziyarce shi ne domin a yi sulhu.

A karo ta biyu Femi Adesina ne ya jagoranta tawagar fadar shugaban kasan, sai dai kash, Sowore ya ce ba zai gana da su ba saboda a cewarsa kotu ta bada belin sa amma gwamnati taki bin wannan umarni.

Share.

game da Author