Yadda dan majalisar Madobi ya daure dalibin jami’ar Bayero saboda sakon Facebook

0

Har yanzu dai matashin dalibin nan dake karatu a Jami’ar Bayero dake Kano, Yahuza Tijjani na nan tsare a gidan kaso a dalilin wai ya yi rubutun suka ga wani dan majalisa dake wakiltar Madobi a majalisar jihar Kano.

Dan majalisar, Kabiru Ismaila ya zargi Yahuza da yin rubutun suka da cin fuska akan sa a shafinsa na Facebook.

Honarabul Ismaila bai yi wata-wata ba sai ya yi amfani da karfin kujerar sa ya sa ‘yan sanda suka cafke dalibi Yahuza.

Bayan yan kwanaki da yayi tsare a wurin ‘yan sanda sai aka kai shi kotun dake unguwar (No Mans Land) dake Karamar hukumar Fage, daga nan sai alkali ya daure Yahuza.

‘Yan uwan Yahuza da suka zanta da PREMIUM TIMES sun bayyana cewa suna kokarin ganin an sako Yahuza don ya koma makaranta amma abin ya citura domin ko daga baya da suka samu alkalin da ya yanke hukuncin tun a farko ya fadi musu cewa an maida shari’ar ofishin Antoni Janar din jihar.

” Mun yi ta jigila zuwa ma’aikatar shari’a ta jihar amma a duk sa’adda muka je sai a hana mu ganin kwamishinan. Babban abi da muke tsoro shine kada a sallameshi daga makaranta domin domin ya shafe tsawon lokaci baya zuwa karatu.

An ce Yahuza ya maida da martani ne ga wasu dake goyon bayan shi honorabul Ismaila a Facebook inda ya ce ” gwanin nasu ma bai iya lissafi ba sannan ko makaranta bai yi ba.” A tsakaninsu can a Facebook, amma shine wannan dan majalisar yayi amfani da dama da karfin kujerar sa ya a daure shi .

Kungiyar daliban Najeriya reshen jihar Kano sun yo tattaki bar zuwa ga wannan dan majalisa suka roke shi amma ya ki amincewa da ya bada da dama a sake shi.

PREMIUM TIMES ta samu ji daga bakin shi honorabul Kabir Ismaila, domin jin ko akwai dalilin da ya sa yaki sairaren jama’a da tausaya wa wannan dalibi.

” Yahuza ya ci mini mutunci ne ya. Da naga ba zan iya hakuri ko kuma in yi wani abu da zai saba wa doka ba sai na kai kara ga hukuma domin abi min hakki na. Amma babi wanda zai iya hakura da irin kalaman da wannan yayi a kai na.

Share.

game da Author