Yadda babban hafsan soja ya danne kudaden gina asibitoci da makarantu

0

Kallo ya koma sama a Babbar Kotun Tarayya da ke shiyyar Maitama, Abuja, inda a ranar Alhamis wani mai gabatar da shaida ya fallasa yadda Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama, Umar Dikko ya yi rub-da-ciki a kan wasu bilyoyin kudade.

Daga cikin bilyoyin kudaden da mai bayar da shaida Hammadama Bello ya bayar, har da bayani dalla-dalla a kan yadda Dikko ya danne naira bilyan 1.2, na kudaden da aka ware domin gina makaranta a barikin sojan sama na Kano, gina asibiti a Yola, Kaduna da Kado, Abuja da kuma kudaden aikin gyaran barikokin sojojin sama.

Hammadama Bello, shi ne mai shaida na 9 da EFCC ta gabatar, ya shaida wa kotu cewa Umar Dikko ya karkatar da kudaden ya gina katafaren gida a cikin Maitama, Abuja, wanda akalla zai kai naira bilyan 1.2.

A matsayin Dikko na babban hafsan hafsoshin sojojin sama a lokacin sa, shi ya rika bugun kirjin bayar da umarnin a cire ko a debi kudade ga babban jami’in kula da kudaden bangaren ayyukan sojojin sama.

Mai shaida Bello ya ce Bukar Abubakar sunan jami’in kula da harkokin kudaden.

A bajekolin zargin satar da aka yi wa Umar Dikko a kotu, an nuna cewa ana zargin sa da harkallar naira bilyan 9.7, kudaden da aka ce akalla sai ya yi shekara 250 ya na rike da mukamin babban hafsa kafin albasshin sa da alawus din sa su tara masa wadannan makudan kudade.

Sannan kuma mai gabatar da shaida har ila yau ya bada shaidar yadda Dikko ya rika jidar naira milyan 558 a kowane karshen wata daga kudaden rundunar sojojin sama Najeriya, a lokacin da ya ke babban hafsan ta.

Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na EFCC ya bayar, ya kara da cewa Mai Shari’a Nnamdi Dimgba sai ya sallami mai gabatar da shaida, sannan ya umarci a ci gaba da shari’a washegari, wato a jiya Juma’a.

PREMIUM TIMES HAUSA za ta kawo muku yadda ta kaya a kotun a jiya Juma’a.

Share.

game da Author