Yayin da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya na bukatar kudaden da zai fara gagarimin aikin magance rikicin makiyaya da manoma a farkon wannan shekarar, ba shi da masaniyar cewa wani gazagurun mai-fada-a-ji zai shantale masa kafafu har a karshe a kwace shirin daga hannun sa.
To abin da dai ya faru kenan yayin da Osinbajo ya aika da takardar neman amincewa a ba shi kudaden aiki, sai ta kasance Abba Kyari, wanda shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya yi masa zagon-kasa.
Bayan da Kyari ya yi nasarar da ya zuga Buhari ya fasa bai wa Osinbajo kudaden fara aikin gina Ruga, sai kuma ya sa Buhari ya cire shi daga Shugaban Kwamitin Sasanta Rikicin Fulani da Makiyaya, wanda aka dora wa ayyukan gina rugage.
PREMIUM TIMES ta samu wannan tabbacin daga wasu takardun bayanai da za ta iya kafa hujja da su, da kuma hirarrakin da ta yi da wasu mutanen da ke da kusanci da kuma masaniyar kwatagwangwama, kutunguila da annamimancin da ke wakana a Fadar Shugaban Kasa.
Wadannan takardun bayanai na Musamman da yanzu haka kwafen su ke a hannun PREMIUM TIMES, karara sun a nuna irin wulakanci da tozartawar da Osinbajo ke fuskanta, a daidai lokacin da a fadin kasar nan ake ta watsa ji-ta-ji-tar cewa makusantar shugaban kasa su na yi wa Mataimakin sa Osinbajo kallon-hadarin-kaji.
Takardun Neman Amincewar Shugaba Buhari
Takardun wadanda ke hannun PREMIUM TIMES su nuna cewa Osinbajo ya rubuta wa Buhari takardar tsarin yadda za a yi aikin na NLTP har gida uku ko kashi uku.
Dama kuma tun farko Buhari ne da kan sa ya nada Osinbajo cewa shi ne zai jagoranci shirin tare da gwamnonin kasar nan.
A ranar 12 Ga Afrilu, 2019, Osinbajo ya rubuta takarda zuwa Ofishin Shugaban Kasa, inda ya rubuta bukatar naira bilyan 35, wadda daga cikin kudin har an rigaya an sakar masa su domin aikin gina matsugunan Fulani da za a gina musu ababen more yaruwa a ciki. Tare kuma da shata musu wuraren kiwo.
Kudaden dai an shirya daga kudaden tallafin zaizayar kasa na gwamnonin kasar nan za a fitar da su.
An ware naira bilyan 12 domin aikin gina rugage a jihohin Nasarawa, Niger, Zamfara, Kebbi, Kogi, Adamawa, Benue, Kaduna, Katsina da Taraba.
Wadannan jihohi ne aka amince cewa su ne a sahun gaban inda rikicin makiyaya da manoma ya fi yi wa mummunan ta’adi.
Ganin tunda har an rigaya an saki naira bilyan 12 daga cikin kudin, sai Osinbajo ya roki Buhari a sakar masa cikon naira bilyan 22 domin ci gaba da ayyukan raya yankunan musamman har da jihar Filato da sauran inda rikicin ya fi muni sosai.
Wasikar mai lamba SH/VP/NLTP/02/1, ta nuna cewa a zuba kudin cikin nwani asusu da ke Babban Bankin Tarayya, CBN.
‘Gogan Hana Ruwa Gudu’
Maimakon Kyari ya mika wa Buhari wannan wasika ta Osinbajo, sai ya rike ta ofishin sa sama da wata daya, sai a ranar 16 Ga Mayu sannan ya ba shi. Kafin ya damka masa wasikar, sai da Kyari ya yi nazarin ta, sannan a gefe ya yi ma ta kaca-kaca da rubutun na sa ra’ayin da kuma shawara ga Shugaba Buhari.
Rijiya Ta Bada Ruwa, Guga Ta Hana Diba
Kyari ya rubuta wa Buhari cewa kada ya amince a bai wa Osinbajo cikon naira bilyan 22, saboda bilyan 12 din da aka rigaya aka damka masa ma, babu wani aikin a zo a gani da ya gudanar da su.
Ya kuma kara da cewa akwai wani dalili da ya hada cewa:
“Shirin na Ruga ba zai yi wani tasiri a yanzu ba, domin an maida batun rikicin makiyaya da manoma a cikin Shirin Majalisar Samar da Abinci ta Kasa, wadda Shugaban Kasa ke shugabancin ta.” Haka Kyari ya rubuta wa Buhari.
Daga nan sai Kyari ya ci gaba da zayyana wa Buhari cewa kawai ya rushe shirin Ruga, ya karbe aikin daga hannun Osinbajo.
Maimakon Ruga, sai Kyari ya shawarci Buhari ya kafa Hukumar Inganta Kiwon Dabbobi da Kifi na Kasa.
A ranar 24 Ga Mayu, sai aka wayi gari Shugaba Buhari ya amince da dukkan shawarar da Abba Kyari ya ba shi.
“Na amince da shawarwarin da ka ba ni.” Haka Buhari ya rubuta, kuma sa hannu ya maida wa Kyari, a cikin wasikar sa mai lamba PRES/65-I/COS/2996.
Ganin yadda Buhari ya amince da Shawarar Kyari ba tare da ya tuntubi Mataimakin sa Osinbajo ba, hakan na nuni da cewa shugaban kasa ya fi ya fi ganin kimar manyan hadiman sa fiye da Osinbajo mataimakin sa.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa, sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa babu wani dalilin da zai sa Buhari ya dauki wannan matakin, wanda daya ne daga cikin zagon-kasan da ake yi wa mataimakin sa, Osinbajo.
Shi dai Osinbajo ya Buhari Shugaban Kasa ya rubuta wasikar sa kai-tsaye. Ba a san dalilin da zai sa Shugaban Ma’aikatan sa Abba Kyari zai rike wasikar har tsawon wata daya bai aika wa Buhari ba. Sannan kuma babu dalilin da zai yi uwa-makarbiyar yin rubutu a kan wasikar har ya na bada ta sa shawarar.
Wata majiya kuma ta kara da cewa ba aikin Shugaban Ma’aikata ba ne ya yi katsalandan a kan wasikar da Mataimakin Shugaban Kasa ya rubuta wa Shugaban kasa.
Wani jami’i kuma cewa ya yi “Kyari ya murde aikin ne ya maida shi ta ofishin Shugaban Kasa, saboda ya san idan Buhari ke jagorancin aikin, to zai rika bayar da umarni a madadin shugaban kasa. Ciki kuwa har da kashe kudade kai-tsaye, ba kamar idan aikin ya na hannun kwamitin Osinbajo ba.”
Manyan jami’an yada labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu da Femi Adesina ba su amsa bayanan da PREMIUM TIMES ta nema daga gare su ba.
Mataimaki Ko Saniyar-Ware?
Wani masanin harkokin siyasa mai suna Sola Olubanjo, ya bayyana matsalar kutunguila da algungumancin da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa, inda ya buga ma ta misalin cewa:
“Muddin Shugaban Kasa ya na haba-haba da kai, to ko da kai kukun da ke dafa abinci ne ko mai wanki da guga, za ta iya taka mataimakin shugaban kasa kan ka tsaye.”
Cikin makon da ya kamata, Buhari ya tafi London hutun kwanaki biyu. Kuma a can Abba Kyari ya bi shi inda ya kai masa kwafen Dokar Yarjejeniyar Raba Ribar Danyen Mai, ya sa ma ta hannu.