Da alama wa’adin dan wasa Cristiano Ronaldo a kungiyar Juventus ta birnin Turin a Italy ya kusa zuwa karshe, domin ya nuna ba zai yi tsowon lokaci a kulob din ba.
Ronaldo ya bai wa duniya mamaki a jiya Lahadi, yayin da ya fice daga sitadiyan ya yi tafiyar sa zuwa gida, bayan an cire shi a daidai minti na 55.
Ronaldo bai ji dadin cirewar wa, inda ya shige ta hanyar karkashin kasa ya nufi gida kai-tsaye.
An maye gurbin sa ne da Paulo Dybala, wanda a daidai minti na 77 ya jefa kwallon da ta yi sanadiyyar yin nasara a kan AC Milan. Wannan canji ya yi daidai kenan, ganin cewa tun da aka fara wasan Ronaldo bai tabuka komai ba.
Cirewar da kociya Maurio Sarri ya yi wa Ronaldo ta bakanta masa rai. Dama kuma a cikin makon da ya gabata, an cire shi a wasan Champions League ana saura minti 10 a tashi wasa. A nan ma ya nuna fushin sa, ganin cewa rabon da a cire shi a wasan Champions League kafin a tashi, tun cikin 2016 a lokacin ya na Real Madrid.
Babu Sauran Bijinta a wurin Ronaldo
Tsohon dan wasan Juventus kuma tsohon kociyan kulob din, Pabio Capello, ya bayyana cewa an shafe shekara uku cur Ronaldo bai yanke dan wasa ko daya ya wuce da kwallo ba.
Ya yi wannan ikirari ne a hirar da ya yi jiya Lahadi da gidan talbijin na Sky Sport Italia, bayan Ronaldo ya fice daga filin wasa ya tafi gida kafin tashi kwallon da Juventus ta buga da AC Milan a Turin.
Capello wanda ya taba yin kociyan Real Madrid, ya bayyana cewa yanzu kwallo ta fara sakin kafafun Ronaldo, ya daina kazar-kazar da azargagen yanke dan wasan da aka san ya kware ya na yi sosai a baya.
“Rabon da Ronaldo ya yanke dan wasa ya wuce an kai shekaru uku kenan. Sai dai zari-ruga kawai ya ke yi. Wanda a da kuwa ba haka aka san shi ba.
“Duk wanda ya san Ronaldon La Liga ai ya san ba shi ne Ronaldon yanzu ba. Na jinjina wa Sarri da ya cire shi ya maye gurbin sa da Dybala. Ga shi yanzu Dybala din ya biya bukata.
“Juventus na da Douglas Costa da Dybala, kuma ko babu Ronaldo su na ci ma ta kwallaye.” Inji Dattijo Capello.
Shi kuwa kociya Sarri cewa ya yi Ronaldo ya yi kokari domin ya buga wasan ne alhali bai gama warkewa garas daga raunin da ya ji ba.
“Irin wannan fushi da Ronaldo ya yi ai ba wani abu na ne. ‘Yan wasa dama sun saba irin haka idan an cire su a lokacin da ba su so a cire su din ba.”