Tun ina da shekaru 16 na yi aure sannan ko makarantar Firamare ban yi ba – Uwargidan Gwamnan Bauchi

0

Uwargidan gwamnan Bauchi, Aisha Mohammed ta yi kira ga iyaye da su rikabtura ‘ya’yan su makarantar Boko.

Aisha tayi wannan kira ne a taron ‘Naija Youth Talk’ wanda matasa da ke aiki da hukumar UNICEF suka shirya a garin Bauchi.

Aisha wadda ta yi jawabi a wannan taro ta bayyana cewa ita kanta daga baya ne ta yi karatu.

” Tun ina shekara 16 aka yi min aure, ko makarantan firamare ban yi ba. Ina tare da mijina har saida na haifi ‘ya’ya uku tukunna. Daga nan ne fa mijina ya dauka min malami a gida yana koya min karatu.

” Bayan haka na ne na shiga makarantan sakandare, ga shi yanzu har na kammala digirina a jami’ar Abuja.

Aisha tace dole ne sai an rika yi wa iyaye wa’azi game da muhimmancin saka ya mace a makarantar Boko.

” Mutanen mu basu yarda da haka ba. Za ka ga mutane basu yarda su saka yayan su mata a makarantar boko. Cewa suke saka ‘ya’yansu a makarantar Boko hasara ce kawai. Yarinya tun tana karama sai kaga an an yi mata aure.

Daganan kuma sai tayi kira da a daina dogaro da aikin gwamnati kowa ya kama sana’a.

” Daya daga cikin ‘yayana duk da gata dayake da shi, ya shiga harkar noma. Kullum yana gona. Haka kuma daya daga cikin ‘ya’ya na mata tana sana’ar girke-girke.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, ya kara da cewa

Share.

game da Author