TSOMOMUWA: ‘Oshiomhole ya sauka kawai’ – Inji Kungiyar gwamnonin APC

0

Rikicin da ya tirnike jam’iyyar APC mai mulki ya kara tirnikewa da kaurin hayaki, yadda har ta kai Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin APC, ya yi kira ga Shugaban APC, Adams Oshiomhole cewa ya sauka daga shugabancin kungiyar.

Dama kuma a ranar Laraba din wasu shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Edo, mahaifar Oshiomhole, sun rattaba sa hannun dakatar da shi daga APC. Cikin wadanda suka halarci taron har da Gwamnan Jihar Edo din, Godwin Obaseki.

A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin na APC, Salihu Lukman ya fitar, a yau Laraba a Abuja, ya nemi shugaban ya kira taron Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar ko kuma ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.

“Ko dai Oshiomhole ya kira babban taron shugabannin zartaswar APC domin a tattauna matsalar da ta dabaibaye jam’iyyar, ko kuma ya amince da cewa ya kasa jan ragamar APC, ya gaggauta sauka kawai.” Inji Lukman.

“Rabon da a yi taron Shugabannin Zartaswar tun cikin watan Agusta, 2018. Saboda rikita-rikitar da ya ke janyowa an wayi gari Kwamitin Gudanarwar APC ya kankane aikin da ya kamata Kwamitin Zartaswa ne ya kamata su rika yi.

Su kan su din duk sun zama shirim-ba-ci ba. Domin Mataiamakin Shugaba na Kasa, Niyi Adebayo, a yanzu Minista ne na wasanni.

KARANTA: Jam’iyyar APC ta “dakatar” da Oshiomhole

“Sannan kuma akwai rudu sosai, domin Mataimakin Shugaba na Arewa, Lawal Shuaibu an dakatar da shi. Haka nan kuma an dakatar da Mataimakin Shugaba na Arewa Maso Yamma, Inuwa Abdulkadir.”

Ya kara da cewa an dakatar da Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun.

“Shin me ya sa duk aka yi sake hakan ke ta faruwa? Don me ba za a kira taro ba, kamar yadda dokar jam’iyya ta ce a rika haduwa bayan watanni hudu ana tattauna kalubalen da ke fuskantar jam’iyya?

Lukman ya ce Oshiomhole ba ya tabuka komai wajen kokarin ganin jam’iyyar APC ta ci gaba, sai ma jefa jam’iyyar cikin rigingimu da ya dade ya na yi.

Jam’iyyar APC ta dakatar da shugaban jam’iyyar na Jihar Edo

Bayan sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na Kasa da jam’iyyar APC ta jihar Edo ta yi a ranar Talata, a yammacin Larabannan ne uwar jam’iyyar daga Abuja ta sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar Edo.

Kakakin jam’iyyar APC na Kasa, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa, tun bayan aiko da takardar dakatar da shugaban da wasu ‘ya’yan jam’iyyar su 11 suka yi, uwar jam’iyyar ta zauna domin duba wannan takarda.

” Ina so in tabbatar muku cewa wannan takarda ya iske kuma mun duba shi. Jam’iyya ta yanke hukuncin amincewa da dakatar da shugaban APC na jihar Edo.

Lanre ya ce wadanda suka dakatar da shugaban sun bi yadda yake a dokar jam’iyyar.

Sai dai kuma shi shugaban ya yi watsi da wannan matsaya na uwar jam’iyyar. Ya ce bata isa ta dakatar dashi ba sai an yi zama ta musamman da jiga-jigan jam’iyyar sannan an rattaba hannu kafin dakatar dashi ya tabbata, kuma ba ayi ba.

Share.

game da Author