Tsohon gwamna Yari na yi wa harkar tsaro zagon kasa a Zamfara – Inji Matawalle

0

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle, ya zargi tsohon gwamnan da ya gada, Abdul’aziz Yari da hannu wajen yi wa harkar tsaron jihar Zamfara zagon kasa.

Gwamnan ya yi wannan zargi ne ta hannun Kakakin Yada Labarai na gwamnan, Yusuf Idris.

Idris ya fitar da sanarwa, wadda ya sa wa hannu a madadin Matawalle cewa, Yari da magoya bayan sa na jinnhaushi da kishin irin zaman afiyar da aka samu a Jihar Zamfara, a karkashin Matawalle.

Ya ce an cimma yarjejeniyar samar da zaman lafiya tare da maharann da suka addabi jihar shekara da shekaru, a karkashin gwamnatocin da suka gabata.

“Tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ba ya jin dadin zaman lafiyar da aka samu a jihar Zamfara, shi ya sa ya ke ingiza yaran sa su na yi wa tsaron jihar Zamfara barazana.”

Haka sanarwar ta bayyana a madadin Gwamna Matawalle.

Ya ce tun bayan da Yari ya sauka daga mulki, sau uku ya ziyarci jihar Zamfara, kuma duk zuwan sa sai rashin zaman lafiya ya biyo baya.

Ya ce akwai abin daure kai idan aka yi la’akari da jama’ar da Yari ke tarawa, wadanda taron na su ba bisa abin da doka ta gindaya ake gudanar da shi ba.

Daga nan sai Matawalle ya kara da cewa gwamnati za ta dauki kwakkwaran mataki a kan ko ma wa aka samu ya na watsa karairayi da watsa hotunan karya a soshiyal midiya dangane da al’amurran jihar Zamfara.

“A yanzu haka ina kan sake fasalin jami’an tsaro a jihar Zmafara domin a damke tare da gurfanar da duk wadanda aka kama suna wannan aika-aika. Duk girman mutum, kuma duk mukamin sa ko wace kungiya ya ke a cikin al’umma.”

Yayin da PREMIUM TIMES ta kasa samun Yari ko kakakin sa Ibrahim Dosara, domin jin karin bayani daga gare su.

Share.

game da Author