Wannan rubutu ya samo asali ne daga korafe-korafe ko koke-koken da maza ke yi a kan kayan lefe a al’adar Bahaushe. Al’ada ce mai karfi yin kayan lefe ga amarya, ba ga Hausawa kadai ba, har ma da kabilu daban-daban a kasar nan.
A batutuwa da dama za ka ji Hausawa na kuka da tsadar lefe. Ko kuma ka yi mai neman aure na susar keya, ya na jinjina kudin da zai kashe, ko kuma wadanda zai shiga cikin rana ya share gumi, ya nemo domin hada kayan lefe.
Wannan korafe-korafe har ta kai su kan su wasu malaman addinin Musulunci na yin kiraye-kirayen cewa a rika saukake shi idan hakan ta kama.
To akwai abin dubawa da dama dangane da batun lefe kafin a zo kan kayan daki, irin su gado, kujeru da sauran kayan alatun da ake cika dakin amarya da su?
KO YA DACE malamai da sauran masu cewa a rika saukaka kayan lefe ko a soke lefe su rika yada wannan ‘fatawar’ ba tare da yin la’akari da sauran abubuwa ba?
Yaushe wanda zai nemi auren budurwa ko bazawara ya ce ya kasa yi ma ta lefe, amma kuma shi lallai auren ya ke so?
Idan aka kawo maka amarya ba tare da ka yi ma ta lefe ba? Mahaifin ta ka ke so ya yi ma ta kayan da za ta rika sawa a gidan ka kai ango?
Me ya sa ba a bayar da ‘fatawar’ cewa iyayen amarya su daina yi ma ta kayan daki irin su gado da kujeru da sauran su? Shin wa shari’a ta ce ya tanadi wurin zama da wurin kwanciya da kayan kwanciyar? Ango da zai yi aure ko kuwa iyayen amarya?
Na san al’adu da dama wadanda ango ne zai bayar da kudin da amaryar sa za ta sayi kayan daki, har da kayan gado da kujeru da sauran su.
Al’adar Fulani na yankin kewayen garuruwan Abuja, kafin ba aurad da budurwa sai an kai shanu rikakku wanda sun kai shekara daya da haihuwa har guda uku. Wasu ma fiye da haka.
Ba na so na kawo irin hidimar da ango dan kabilar Igbo keyi kafin ya auri mace. Don kada a ce ai su ba layin mu daya ba.
Amma dai kamar akwai tantagaryar rashin adalci karara ga iyayen amarya a bar su da gaganiyar neman kudin yi wa yarinyar su kayan gado, kujera, kwaba na zuba kaya, kayan kicin na dafa abinci, wadanda a shari’a duk ango ne ya kamata ya tanadar wa amarya sa su. Sannan kuma a koma ana neman a saukake wa ango kayan lefe.
Ya wanda ya kasa hada kayan lefe zai iya kulawa sosai da macen da ya aura amma kuma ba ya iya sai ma ta zannuwan daurawa da kayan kwalliya?
Ya kuma mai irin wannan tunanin ko wanda ya kasa samar da wadannan kayan a al’adance kuma ya zura idanu iyayen amaryar sa ku tatike aljifan su da ajiyar su da bankin su da rumbun su don su sayi kayan gado da kujerin da mijin ‘yar su da aka aura zai rika kwantawa ya huta?
Wannan wane irin tunani ne haka?
Wato a bisa alama fa shi namiji bai damu ba idan aka ce a daina lefe kwata-kwata. Amma kuma ba zai yarda ba idan aka ce iyaye su daina yi wa ‘ya’yan su mata kayan daki. Ba zai ji dadi ya shiga dakin matar sa ya iske babu gado da kujeru da kayan alatu ba. Kuma babu kayan kicin da sauran kayan dafa abinci, wadanda idan za a baje shari’a a faifai, to shi mijin ne ma ya wajaba ya tanadar wa amaryar sa wadannan kayan.
Idan mazana zuguguta a saukake musu lefe, su na kara rage wa mace daraja ne. Za su rika yawan auri-saki, saboda sun san ba sai an kashe wasu kudade da yawa kafin a yi aure ba.
Me zai hana idan za a yi adalci a ce har kayan daki ma a daina? Ya rage kenan ga miji ya tanadar wa matar sa wuri da gado da kujerun da za ta kwanta ko ta zauna ta huta.
Amma iyayen amarya sun shafe shekara da shekaru, sun a tanadin kayan daki ‘yar su. Kai kuma ango ka shafe shekara daya ko biyu ka na son ‘yar su da aure. Amma kuma biki ya zo b aka da halin yi ma ta lefe. To aikin me ka ke yi, ko sana’ar me ka ke yi? Anya za ka iya rikon ‘yar mutane da daraja kuwa?
Haba ango! Kai ba za ka yi tanadin kayan lefen da wuri ba, ko ma da ba ka da budurwar da za ka aura, tunda dai ka san za ka yi auren? Kai fa kai kadai ne b aka da nauyin iyalin da ka ke ciyarwa. Amma uban yarinya bai damu da nauyin iyalin da ke kan sa ba. Shi da mahaifiyar yarinya su na ta gaganiyar rufa wa ‘yar su asiri. Kai kuma ka na ta kikiniyar a saukake ma ka kayan lefe. Anya za ka iya sai wa dan ka ragon suna kuwa idan ta haihu shekara daya bayan biki?
KU KUMA MALAMAI me zai hana ku koma ku na magana kan wajibcin wanda ya kamata ya sai wa amarya gado da sauran kayan daki? Ango ne ko kuwa mahaifin amarya. Kun bar iyayen yarinya sun a kashe makudan kudade, sun a wahala da sunan fitar da ‘yar su kunya.
Me ya sa ba a nasihar rage wa iyayen yarinya kashe kudi a lokacin auren ta, sai a yi ta nemar wa ango shi kadai sauki? Irin haka tun ana nemar ma sa sauki, har shi kuma ya fara tunanin cewa a bilis ma zai iya auren budurwa. Kuma zai iya sakin ta bayan wata daya ya sake auren wata ma duk a bilis, domin al’adar Bahaushe ta daure masa gindin ya rika yin aure a bilis.
Ko an ki ko an so, idan ana rage wa mace daraja a gaban angon da zai aure ta, to za a samu yawaitar kasa rikon aure da daraja. Za a iya wayar gari ko daren tuwo amarya ta yi, tuni ango zai iya rubuta ma ta takardar saki, saboda ya san dan albashin sa na wata daya ko biyu ma zai iya auro masa Lantana, Mairo, Naito, Assibi, Jumande, Baraka, Ladidi ko Ta-Annabi ko Zulai ’yar Malam Abashe.
Kai Garbati, gara ma kai da Sulele da Saddi da Alka ku canja tunani cewa Duduwa ’yar Babani fa dankwaleliyar budurwa ce. Ba amaryar-buzuzu ba ce. Ko buzuzu ma kafin ya kai mirgina amaryas sa cikin rami, sai ya yi gumi karcat. Kuma shi kadai ke gaganiyar sa, babu mai taya shi!