Sanata Dino ya sha kayi a karamar hukumar sa, yayi nasara a Yagba

0

A sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayyana a garin Lokoja da safiyar Lahadi, Sanata Dino ya sha kayi a karamar hukumar sa ta Ijumu.

Jam’iyyar APC ta samu zunzurutun kuri’u har 11,627, PDP kuma 7,647.

An soke zabe a rumfunan zabe 5 a dalilin rikici da aka yi a wuraren.

Haka kuma APC ce ta lashe kananan hukumomin Kabba Bunu, inda ta doke PDP da kuri’u sama da 6000.

APC – 15,437, PDP – 8974.

Karamar hukumar Lokoja – APC – 14,168 PDP – 9786.

Moa Muro – APC 4874, PDP – 3704.

Yagba East PDP – 7,745, APC – 6,683.

Share.

game da Author