Sakamakon da ke kara ci gaba da fitowa daga rumfunan zabe da mazabu a fadin jihar Kogi, su na kara nuna cewa jam’iyyar PDP ta tsere wa jam’iyya mai mulkin jihar, APC fintinkau.
Sakamakon dai ya na akwai nuna rata mai yawa da ke jefa fargaba a zukatan wadanda aka tserewa. Gwamna Yahaya Bello na ci gaba da shan kaye warsas a rumfuna da akwatinan zabe daban-daban.
A Karamar Hukumar Idah, Mazaba ta 4, Rumfar Zabe ta PU10, PDP na da kuri’u 205, APC kuma 25.
Haka abin ya ke a Mazabar Ode cikin Karamar Hukumar Yagba ta Yamma. APC na da 74, PDP na da 109.
A Mazabar Omepa, Rumfar Zabe mai lamba PU008, PDP ya samu 361, APC kuma 40.
Ko a Karamar Hukumar Mopamuro, APC na ci gaba da shan kashi, inda ta samu 33 a Mazabar Ofishin ‘Yan Sanda na Orokere, PDP kuma 117.
PDP ta samu yawan kuri’u har 330 a Mazabar Bayan Garin Anka 1, cikin Karamar Hukumar Ankpa. Ita kuwa APC 41 rak ta samu.
A Karamar Hukumar Idah, Mazabar PU007, rumfa ta 07, APC ta samu 38, ita kuma PDP ta na da 216.
Sai Mazabar Islamiyyar Ankpa ta Bayan Garin Ankpa 1 inda APC ke da 45, ita kuwa PDP har kuri’u 336 ta samu.
BI MU KAI TSAYE A NAN: ZABEN KOGI: APC na shan kayi a yankin Kogi ta Gabas, PDP kuma na shan ragargaza a yankin Kogi Ta Tsakiya
Bi nan kai tsaye: https://wp.me/p8iDgo-6sx
Discussion about this post