Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakaci da aiki da ma’aikatan kiwon lafiya ke yi a asibitocin kasar nan ne babban dalilin da ke sa ake fita neman magani a asibitocin kasashen waje.
Buhari ya fadi haka ne a taron kungiyar likitocin Najeriya (NMA) da likitocin kungiyar kasashen rainon Ingila (CMA) suka shirya.
Taron mai taken “Maida Hankali Kan inganta lafiyar mutane, ya samu halartar manyan likitoci da masu ruwa da tsaki a harkar kiwon Lafiyar Najeriya.
Shugaba Buhari wanda ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya wakilta ya ce
“Idan kuka duba za kuga cewa rashin isassun ma’aikata,rashin ingantattun kayan aiki,rashin tsafta a asibitoci,wulakanta marasa lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya ke yi sun isa su kora mutane zuwa kasashen waje.
Ehanire ya ce daraja da kiman fannin kiwon lafiyar kasar nan zai dawo ne idan aka kawar da matsalar.
Ya kuma ce kamata ya yi ma’aikatan kiwon lafiya su kara mai da hankali wajen kula da marasa lafiya tare da wayar da su kan cututtuka.
Daga nan sai kuma tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya ce ficewa zuwa kasashen waje da mutane ke yi na sa a yi asaran kudade masu yawan gaske.
Yakubu ya ce idan ba a manta ba a shekaran 2017 ne tsohon ministan kiwon lafiya Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa akan yi asaran dala biliyan 175 a dalilin ficewar ‘ Yan Najeriya zuwa kasashen waje.
Discussion about this post