Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa masana’antar hada taragon jiragen kasa ta jihar Ogun za ta samar da aikin yi ga matasa kimanin 5,000.
Amaechi ya bayyana haka a lokacin gagarimin taron kaddamar da bude masana’antar da ke Kajola, Jihar Ogun, a ranar Asabar da ta gabata.
A wurin taron, wanda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bude, Amaechi ya kara da cewa za a ci gajiyar masana’antar ne sakamakon wani hadin guiwa da Najeriya ta yi kamfanin gine-gine na kasar Chana mai suna CCECC.
“Domin tabbatar da an cimma kudirin biyan bukatun fasinjoji da kuma kayan su, sai gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar aikin samar da taragai na cdaukar fasinjoji da kuma wagunu na daukar kaya domin saukake zirga-zirgar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna, Itakpe zuwa Ajaokuta zuwa Warri da kuma Lagos zuwa Ibadan.”
Ya kara da cewa kuma zai amfani dukkan harkokin sufurin jiragen kasa da nan shiyyar Afrika ta Yamma.
“Kacokan wannan gagarimin shiri duk aiki ne wanda kamfanin CCECC ya zuba kudin sa da aka cimma yarjejeniya tun cikin 2018.
“Idan aka kammala aikin zai samar da ayyukan yi ga mutane kimanin 5,000, wanda a idan tafiya ta yi tafiya, nan gana masana’antar za ta rika samar da taragan jirage da za a rika amfani da su nan Najeriya da kuma Afrika ta Yamma.
Yayin da ya ke kaddamar da masana’antar, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jinjina wa Ministan Harkokin Sufuri, Amaechi, saboda kokarin sa wajen farfado da harkokin sufuri a Najeriya.
Osinbajo ya ce wannan gagarimin aiki da kuma jajircewar da Amaechi da ma’aikatar sufuri suka yi, ya nuna cewa a yanzu da kuma nan gaba, Najeriya za ta zama gagarabau wajen kawo ci gaba ta hanyar saukaka zirga-zirga a kasar nan, albarkacin bunkasar harkokin jiragen kasa.