Mutanen garin Karaye sun fito zanga-zanga nuna rashin amincewar su da hukuncin Kuto na rusa masarautu hudu da gwamnan jihar Kano Ganduje yayi.
Babbar kotu da ke Jihar Kano karkashin mai shari’a Usman Na’Abba, ta soke sabbin manyan masarautu hudu da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya kirkiro.
Mai’sharia Usman Na’Abba ne ya yanke wannan hukunci a ranar Alhamis a Kano.
Idan ba a manta ba Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta umarci Gwamna Abdullahi Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi cewa kowa ya tsaya matsayin sa, a kan umarcin da kotun ta bayar tun na ranar 10 Ga Mayu.
A waccan ranar dai kotun ta hana a nada sarakunan na Gaya, Bichi, Karaye da kuma Rano.
Sai dai kuma jim kadan bayan yanke wannan hukunci sai mutanen garin Karaye suka fito domin yin zanga-zanga da nuna rashin amincewar su ga wannan hukunci da kotu ta yanke.
A kwalayen da suka rirrike, masu zanga-zangar sun rubuta kalamai kamar “Abarmu a Masarautar mu ta Karaye” da sauran su.
Masarautu guda hudu ne gwamna Ganduje ya kirkiro sannan tuni har an nada sarakunan wadannan masarautu. Daya daga cikin manyan ‘ya’yan tsohon sarkin Kano Marigayi, Ado Bayero, Aminu Ado Bayero ne sabon Sarkin Bichi.








Discussion about this post