RUFE IYAKOKI: Kakar manoman shinkafar Gombe ta-yanke-saka

0

Wasu manoman shinkafa a Jihar Gombe sun bayyana cewa su na ci gaba da samun karin cinikin shinkafar da su ke nomawa, tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakokin ta da kasashen da ta ke makautaka da su.

Rufe kan iyakokin dai ya hana shigo da shinkafa daga kasashen ketare ta kan iyakokin kasar nan, musamman ta Kwatano da Jamhuriyar Nijar da kuma Kamaru.

An rufe kan iyakokin tun cikin watan Agusta, sai dai kuma Gwamnatin Tarayya ta nuna alamun sake budewa a ranar 31 Ga Janairu, bayan da ta gindaya sharudda kwarara guda 10 ga dukkan kasashen da ke makautaka da ita.

Buhari ya bayyana a cikinn watan Agusta a taron Inganta Tattalin Arziki da aka gudanar a Tokyo, Japan cewa Najeriya ta rufe kan iyakokin ne saboda gagariminn sumogal din kayayyaki da ake yi cikin kasar, ba tare da gwamnati na amfana da makudan kudaden shiga ba.

Wani binike da wakilin mu ya yi, ya gano cewa bayan rufe kan iyakoki, manoman shinkafa sun fito da sabbin dabarun sheke shinkafa su gyara ta, su na durawa a cikin buhunna, da nufin inganta su.

Manoma da dama sun bayyana cewa rufe kan iyakoki da Shugaba Buhari ya bayar da umarni, ya zama abin alheri a gare su da kuma bunkasar harkar noma a kasa baki daya.

Sun ce yanzu su na noma shinkafa mai yawan gaske, saboda yadda bukatar ta ke ci gaba da karuwa.

Tsohon Shugaban Kungiyar Manoma Shinkafa na Jihar Gombe, mai suna Umar Na-Abu ya tabbatar wa wakilinmu da haka. Ya ce tsarin wani mataki ne mai kyau da zai inganta da bunkasa harkokin noma a kasar nan.

Ya ce Najeriya na da karfin da za ta iya ciyar da kan ta, ba sai an dogara da shigo da kayan abinci daga wata kasa ko wasu kasashe ba.

“A da can baya mun yi watsi da wannan wurin, amma yanzu mun dawo kuma a kullum za mu iya gyara buhun shinkafa 10,000.

“Saboda ina da injin casa da gyara shinkafa, a yanzu a kullum ina gyara akalla buhu 1,200. A da can baya kuwa bai fi na gyara buhu 50 kacal a kowace rana ba.

“Mu na sayar da duk buhu daya naira 13,000 zuwa 14,000 har 15,000. Yanzu kuma mu na ta samar wa dimbin matasa ayyukan yi ta hanyar raba su da zaman-kashe-wando a kan titina.” Inji Na-Abu.

Shi ma Abubakar Mohammed cewa ya yi tun bayan da aka rufe kan iyakoki, sai harkokin sa na sana’ar shinkafa ke ci gaba da bunkasa a kullum. Har ta kai sai kara daukar matasa aikin gyaran shinkafa ya ke ta yi.

Shi kuwa Auwal Abari, mai sana’ar sayen shinkafa ya na lodawa a motoci daga Gombe, cewa ya yi “idan ma kan iyakokin Najeriya za su kasance a rufe har nan da shekaru biyar masu zuwa, to Najeriya za ta iya ciyar da kan ta.”

“Ni babban dan sarin shinkafa ne daga Gombe ina kaiwa Lagos, Enugu, Aba da Fatakwal har da Oyo. Kuma daga garuruwa sai mutane ke ta kira na, su na bukatar na rika lodawa ina kai musu. Shi ya sa ni a yanzu ina alfahari da wannan sana’a ta sayar da shinkafa.”

Ya shaida cewa a kullum ya kan biya leburori naira 100,000 kudin aiki, wanda a baya kuwa bai fi ya biya naira 5,000 ga leburori ba.
Hakan inji shi alama ce da ke nuna cewa yanzu harkar noma da sana’ar sayar da shinkafa na ci gaba da bunkasa a Najeriya.

Share.

game da Author