RUFE IYAKOKI: Jami’an Kwastan sun kwace motoci 55

0

Jami’an kwastan a tashar kan iyakar Seme da ke tsakanin Najeriya da Kwatano, sun bayyana cewa sun kama motocin da aka yi sumogal din su zuwa cikin kasar nan har guda 55 tun daga lokacin da aka kulle kan iyakoki, ranar 20 Ga Agusta, zuwa yau.

Kakakin Kwastan da ke Seme, Abdullahi Hussaini ya ce kwace wadannan motoci na daya daga cikin gagarimin nasarorin da kwastan suka cimma a yaki da masu fasa-kwaurin motoci zuwa cikin kasar nan.

“Rundunar kwastan ta kawace motoci 55 wadanda aka shigo da su cikin kasar nan, ba tare da an biya musu kudaden haraji ba, Kudaden motoci ya kai makudan milyoyin nairori.”

Daga nan sai Hussaini ya ce karairayi ne kawai ake yadawa a soshiyal midiya wai jami’an kwastan na karbar kudade wajen ‘yan sumogal su na barin su na shigowa da motoci ta hanyoyin fasa-kwauri.
.
Ya kalubalanci jama’a cewa duk mai wata kwakkwarar hujjar jami’an kwastan sun karbi wurin wani ko wurin sa, to ya gabatar da ita, domin a hukunta wadanda suka karbi kudaden.

Sai ya shawararci masu yada ji-ta-ji-ta a soshiyal midiya su rika bincike kafin su kai ga watsa bayanai marasa tushe balle makama.

Kuma ya ce watsa irin wadannan bayanai ya na kashe wa jami’an kwastan gwarin guiwa.

A karshe ya ce Hukumar Kwastan ta shigo da tsarin rage wa masu sumogal din motocin da aka kwace, kudaden haraji, yadda za su iya su karbi motocin su.

Ya ce duk wadanda aka kwace wa motoci za su iya garzayawa ofishin jami’an kwastan da ake biyan kudade domin su biya harajin kwastan su karbi motocin su.

Share.

game da Author