Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya bayyana cewa zaben da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kogi an yi adalci, sahihin zabe ne, kuma babu magudi.
Ya ce duk da rahotannin da aka rika watsawa cewa an yi tashe-tashen hankula, hakan ba zai sa a rika kushe zaben ba.
Bello ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels, mai suna Sunrise Daily, a yau Talata.
Ya ce ya amince cewa akwai tashe-tashen hankula a lokacin zaben, amma kuma ya kara da cewa hakan bai zama abin kafa hujja har a rika kushe zaben ba.
Bello ya ci gaba da cewa ba a gudanar da wani magudi a yayin zaben ba, an bai wa kowa ‘yancin ya zabi wanda ran sa ke so, Kuma an yi wa kowa adalci.
“Ai dama a kowane zabe za ka samu cewa wani dan abu haka dai ya faru ko ta wace hanya. Amma kuma don wani dan abu ya faru, ai ba zai iya zama wani ma’aunin da za a auna, a yi wa dukkan zaben kudin-goro, a ce ba sahihi ba ne.” Inji shi.
“Idan muka koma kan kungiyoyin rajin dimokradiyya kuwa, ai suna da ‘yancin fadin abin da ran su ke so. Amma kuma kamata ya yi mu san daga wace alkibla su ke auna inganci ko rashin ingancin zaben.
“Rumfar zabe nawa suka je daga cikin rumfuna 2,548, Mazabu 239 kuma Kananan Hukumomi 21? Mutane nawa suka tuntuba?
“Shin sun ma yi hira da dukkan wadanda suka jefa kuri’a ne?
“Don haka da wane irin ma’auni suka auna zaben har suka gane ba sahihi ba ne?
Bello ya yi wannan ikirarin bayan an yi ta bayar da rahotannin yadda aka yi rikice-rikice, satar akwatu da baddata alkaluman zabe da kuma kashe-kashe a Jihar Kogi.