RIKICIN APC: ‘Yan ta-kife sun sheka wa masu zanga-zangar neman a cire Oshiomhole ruwan duwatsu

0

Wadansu gungun masu zanga-zanga dauke da kwalaye sun fito suna nuna bukatar a tsige Shugaban Jam’iyyar APC, Adam Oshiomhole daga mukamin sa na shugabancin APC.

Masu zanga-zangar sun je kofar Hedikwatar APC da ke Wuse, Abuja, dauke da kwalayen da aka yi wa rubuce-rubucen neman a cire Oshiomhole.

Wasu kwalayen na dauke da kakkausan kalamai da suka hada da “Tilas Oshiomhole ya sauka.”, akwai kuma “Barawo” da sauran su.

Masu zanga-zangar wadanda akasarin su matasa ne, sun hadu da fushin wasu ‘yan baberiya, wadanda suka yi musu takakkiya, inda suka rika antaya musu ruwan duwatsu da sanduna, domin ko tarwatsa su.

Akalla an tabbatar da raunata wani matashi daya, a rincimin da ya auku a Abuja.

Wani mai suna Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa shi dan jam’iyyar APC ne, kuma daya daga cikin jagoran masu zanga-zanga.

Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa makasudin shirya zanga-zangar dai shi ne domin su nuna rashin jin dadin yadda Oshiomhole ke shugabancin APC.

“Sakon da mu ke son isawar wa ba wani abin boye ba ne. Abin da kawai mu ke so shi ne Oshiomhole ya sauka kawai. Ba ya amfani da diflomasiyya ya na warware matsalar da ta kunno a jam’iyya. Wannan kuwa ya sa mun rasa jihohi da dama irin su Oyo, Bauchi, Zamfara da sauran su.” Inji shi.

“Abin da ya faru a Zamfara ya bata mana rai sosai. Saboda mu ne muka ci zabe, tun farko amma kotu ta kwace ta bayar wa PDP, saboda Oshiomhole ya dagula al’amarin”

Daga nan sai ya kara da cewa nasarar da jam’iyyar APC ta samu kwanan nan a zabukan gwamnonin Bayelsa da Kogi, ba ta hana a boye cewa har yanzu APC na cikin tsakun rikice-rikice da dimbin matsaloli ba.

’Yan sanda dai tarwatsa wadanda suka rika jifa da barkonon tsohuwa. Kuma kowa ya kama gaban sa.

Share.

game da Author