Kotun dake Mapo a Ibadan jihar Oyo ta raba auren Rukayat Adedoja da mijinta Afeez a dalilin rashin jituwa da suke yawan samu da rashin haihuwa.
Alkalin kotun Ademola Odunade yace ya raba wannan aure ne a dalilin rashin zaman lafiya da yaki ci yaki cinye a tsakanin wadannan ma’aurata.
Odunade ya kuma hori masoya da su rika bincikan halayyar juna kafin su yi aure. Kada su bari dadin ‘I Love You – I Love You’ ya rika dauke musu hankali sai bayan an yi aure kuma sai zama ya gagara.
Kafin alkali ya yanke wannan hukunci Rukayat ta ce roke shi tun farko da ya raba aurenta da Afeez cewa ya ishe ta da gorin rashin haihuwa.
“Afeez kan lakada mun dukan tsiya a duk lokacin da muka yi fada sannan kulum sai ya yi mun gorin rashin haihuwa. Sannan Afeez na kaurace min wajen jima’I.
A nashi bayanin Afeez yace ya yarda da bukatar Rukayyat da a raba auren kawai kowa ya huta.
“Aikin maigadi nake yi sannan duk da haka ina kashe kashi 95 bisa 100 na albashi na a kanta duk wata.
“Rukayat na da sana’o’I guda uku da na bude mata wanda take samu daga ciki amma haka bai hana Rukayat barin gidana ba har na tsawon watanni uku ta taci yawon holewarta.