Kungiyar malamai da manyan ma’aikatan manyan makarantu mallakan gwamnatin jihar Kaduna sun sanar wa gwamnatin jihar cewa zasu fara yajin aiki muddun ba ta inganta albashin malamai da ma’aikatan makarantun ba.
Shugaban gamayyar kungiyoyin na hadin guiwa Noah Dallami ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa kungiyoyin sun ba gwamnati wa’adin kwanaki 21 ta duba wannan kuka ta su domin share musu hawaye.
Baya ga inganta albashi, kungiyoyin sun koka da rashin kayan aiki da ingantattun wuraren koyarwa da suke fama da su.
” Akalla shekaru 10 kenan muna fafatawa da gwamnati tun daga na baya har zuwa yanzu amma shiru kake ji. Da wannan gwamnati ta zo mun yi ta ganawa domin ko za mu samu dacewa amma ina. Wannan shina abinda ya fi dacewa muyi ko gwamnati zata saurare mu da gasken gaske ta share mana hawaye.
Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Shehu Makarfi ya yi kira ga kungiyoyin su yi hakuri su kara ba gwamnati lokaci.
” Mun dade muna tattaunawa da kungiyoyin malamai domin kawo karshen wannan matsala da muka gada. Muna rokon su da su ci gaba da hakuri da gwamnati sannan su zo mu ci gaba da zama a teburin tattaunwa domin kawo karshen wannan matsala domin ci gaban jihar” inji Makarfi.