RAHOTON BINCIKEN NDHS: Duk da matsalolin da ake fama da su a fannin kiwon lafiyar Kasar nan an samu ci gaba matuka

0

Sakamakon binciken hukumar NDHS ya nuna cewa an samu ci gaba matuka a fannin kiwon lafiyar Najeriya sai dai kuma har yanzu akwai matsalolin dake haddasa koma baya a fannin.

Sakamakon ya kara nuna cewa wadannan matsalolin dake haddasa koma baya a fannin ba sabbin matsaloli bane sun dade sun gurgunta harkokin kiwon lafiya a kasar nan.

Jami’ar gwamnatin kasar Amurka Kathleen FitzGibbin ta bayyana cewa amfani da sakamakon wannan bincike da kara ware wa fannin kudade zai taimaka wajen samun ci gaba matuka a fannin kiwon lafiyar Najeriya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa gwamnati ta yi nasara wajen wayar da kan mata sanin muhimmancin zuwa asibiti musamman a lokacin da suke da juna biyu.

An gano cewa kashi biyu bisa uku na mata masu ciki na zuwa asibiti yin awo sannan kashi 40 bisa 100 na haihuwa tare da taimakon kwararrun likitoci.

Sai dai kuma har yanzu kashi 59 bisa 100 na mata masu ciki na haihuwa a gida ne.

Sakamakon binciken ya nuna cewa yanzu yara kanana sama da kashi 13 bisa 100 ne suka kammala yin allurar rigakafi sannan wajen jarirai 3 cikin 10 ne mahaifan su ke shayar da su nono na tsawon watanni shida.

A bangaren zazzabin cizon sauro kuma mutane kashi 61 a Najeriya na amfani da gidajen sauro a gidajen su sannan kashi 52 na yara na kwana a a cikin gidan Sauron.

Haka ya nuna cewa an samu nasarar rage yaduwar zazzabin cizon sauro daga kashi 42 a shekaran 2010 zuwa kashi 23 a 2018.

A takaice dai sakamakon binciken ya nuna cewa an samu nasarar rage yaduwar cututtukan zazzabin cizon sauro, ciwon sikila, rashin jini a jikin yara da manya da kuma haihuwan yara da nakasu a jikinsu.

Daga nan dai shugaban hukumar kidaya ta kasa Abimbola Hundeyin ta bayyana cewa gwamnati tare da goyan bayan kungiyoyin bada tallafi za ta zage damtse wajen ganin ta kara yin kokari bisa wannan ci gaba da aka samu a fannin kiwon lafiyar kasar.

Hukumar kidaya ta kasa da bangaren yaki da zazzabin cizon sauro na ma’aikatar kiwon lafiya ne suka gudanar da wannan bincike akan mutane 42,000 a shekaran 2018.

Sannan USAID, Asusun duniya, gidauniyar Bill da Melinda Gates,WHO na cikin kungiyoyin bada tallafin da suka tanadi kudade da sauran kayan akin da aka bukata wajen gudanar da binciken.

Share.

game da Author