Numan-Jalingo: Yadda titunan kasar nan suka ragwargwabe, Daga Kais Daud Sallau

0

NUMAN-JALINGO – Wannan hanya ce ta gwamnatin tarayya wacce ta hada jihar Adamawa da jihar Taraba (Numan Zuwa Jalingo).

Duk lokacin da zanyi tafiya idan har wannan hanya zan bi, wata daya kafin ranan tafiyan ba abinda nake tunawa kamar irin artabon da zanyi da ramuka da kura na wannan hanyar. Wanda wani gurin ma sai kun bar hanya kun shiga daji kafin ku dawo kan hanya.

Babu shakka wannan hanya idan ka bita tsammani zaka yi cewa kabari zaka shiga da ranka.

Kais Daud Sallau

Kais Daud Sallau

Hakan yasa tafiyan da ya kamata ayi cikin awa daya da rabi (1hr 30mins) sai ku kwashe kusan awa hudu (4hrs) kuma tafiya saboda lalacewan hanyar.

Ba shakka lalacewan wannan hanyar ya gurfanar da harkan kasuwancin da ake yi a wannan yankin, hakan ya raunana tattalin arzikin yan Kasuwan da suke harka a wannan hanyar. Domin masu mota basu son bin wannan hanyar wanda ya amince zai bi wannan hanyar kuwa, toh sai ya kusan ninka maka kudin mota. Bayan haka sanadiyar lalacewan wannan hanyar yasa ana samu hadari sosai.

Kuma babban abin takaici shi ne, wannan hanyar kusan shekaru goma ko sama da haka a lalace ya ke. Amma ba gwamnatin da ta damu da ta gyara.

Kira ga gwamnatin tarayya da yan majalisun tarayya kama daga na dattawa zuwa wakilai na jihohinnan guda biyu Adamawa da Taraba da su hada kai domin tabbatar da an gyara wannan hanyar. Domin ba shakka ana cutuwa a wannan hanyar matuka gaya. Duk wanda ya bi wannan hanyar na farko ba zai so ya sake bin hanyar ba sai ya zama mishi dole.

Ba shakka matsalar munanan hanyoyi a abune wanda yan Najeriya suka dade suna koke-koke a kai, wanda kusan akasarin hanyoyin kasarnan suna niman gyara matuka. Walau a sabunta su kokuma a gyara su.

Ko kwanakin baya wadansu matasa a jihar Neja sun fito sunyi zanga-zanga game da matsalar hanya da suke fama dashi a jihar. Suna kira ga gwamnatin tarayya da ta gyara wadannan hanyoyi.

Matsalar lalacewar hanya na daya daga cikin abinda yake kawo yawan hadari a kasar nan, wanda ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi su bada himma domin gyara hanyoyin. Gyara hanyoyin zai rage yawan hadarurruka da ake samu, kuma ya bunkasa tattalin arzikin yan kasa dama gwamnati.

Ya kamata gwamnatin tarayya ta sani cewa maganan dawowa da (Toll Gates) da take yi. Toh fa dole sai ta inganta hanyoyi kafin yaba da ma’ana mai kyau. Domin inganta hanyoyin shi zai ba dan kasa damar biyan abinda aka tambaye shi ba tare da ya ji kamar an zalunce shi ba. Amma idsn za’a bar hanyoyin a yadda suke a lalace, kuma a tare mutum a (Toll gates) a karbi kudin a hanun shi, toh fa dole zai ji wani abu na rashin jin dadi a tare dashi.

Sai kaga ance an bada gyaran hanya, amma sai a shafe shekara da shekaru ba a kammala gyarawa ba. Duk da cewa munsan gyaran hanya ba abune wanda za a yi sa cikin karamin lokacin ba idan ana son ayi inganceccen aiki, amma lokutan da ake yi kafin a gama aikin hanya a kasar nan yana yin yawa.

Allah ya ba mu zaman lafiya. Ya kuma ba shugabanninmu ikon yi mana shugabanci nagari.

Share.

game da Author