Gwamnatin Najeriya ta gindaya sharuddan da tilas sai kasashen da ke makwabtaka da ita sun cika kafin ta sake bude kan iyakokin ta.
A ranar Litinin ne Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama, ya shaida haka bayan tashi daga taro da kwamitin lura da rufe kan iyakokin Najeriya na wuicin-gadi ga manema labarai, bayan tashi daga wata ganawa da suka yi.
Tun cikin makonnin da suka gabata ne dai Najeriya ta kulle kan iyakokin ta, a wani yunkuri da mahukuntan kasar suka bayyana cewa domin inganta tattalin arzikin ta da kuma dakile matsalar shigo da makamai cikin kasar.
Wannan mataki da Najeriya ta dauka dai ya janyo wa mahukuntar kasar tsangwa, musamman ana korafin cewa ya saba wa ka’idojin cnikayya tsakanin kasashen Afrika ta Yamma da kuma Yarjejeniyar da kasashen Afrika suka kulla ta amincewa a gudanar da cinikayya kai-tsaye ba tare da tsawwala wa juna ba.
Sannan kuma farashin kayayyaki sun yi tashin-gwauron zabi, yayin da jami’an kwastam ke ci gaba da bindige masu shigo da shinkafa a kan babura ko kananan motoci, ko da kuwa buhu uku aka kama ka da su.
Sai dai kuma wasu ‘yan Najeriya na maraba da wannan shiri, su na cewa hakan zai kara wa kayan gida Najeriya daraja kuma zai ingiza jama’a su rika sarrafa kayan gida, amimakon dogaro da na kasahen ketare.
PREMIUM TIMES kuma ta ruwaito jami’an Najeriya na cewa rufe kan iyakokin da aka yi ya kara samar da makudan kudaden shiga a aljihun gwamnati.
Kafin a rufe kan iyakokin dai gwamnati ta damu da yadda ba a sauke kaya a tashoshin jiragen ruwan kasar nan, sai dai a rika karkatar da su a tashar jirgin ruwa ta Kwanato, daga can a rika sumogal din su cikin Najeriya ba tare da biyan harajin kwastan ba.
TSAURARAN SHARUDDA 10 KAFIN SAKE BUDE KAN IYAKOKIN NIJERIYA
Ka’idoji da sharuddan da aka gindaya, kamar yadda Ministan Harkokin Waje, Onyeama ya bayyana, sun hada da:
Duk wani kayan da za a shigar daga wata kasa da ke karkashin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), to su kasance ba a farke kwalayen su ba.
Kayan su kasance jami’an waccan kasar sun rako su har bakin kan iyakar shigowa Najeriya. Su damka kayan ga jami’an kwastam na Najeriya kamar yadda kayan su ka fito daga kasashen da aka sayo su, ba tare da an farke kwalayen su ko an yi musu ribage ba.
Najeriya ba za ta amince ta yin kumbiya-kumbiya a wannan tsari ba.
Kayan da ake yi daga kasashen Kungiyar ECOWAS su kasance ingancin su ya kai sharuddan da ECOWAS ta gindaya.
Sannan kuma kayayyakin da za a rika shigowa da su daga kann iyakokin Najeriya, su kasance akasari kayayyaki ne da ake sarrafawa a cikin wadannan kasashe.
Kayan da za a shigo da su daga wasu kasashen da ba na ECOWAS ba, sun kasance ingancin su haura sharuddan na ECOWAS da kashi 30 bisa 100. Saboda kasashen ECOWAS tilas su karfafa cinikayya a tsakanin su.
Dole sai an rushe dukkan wasu manya da kananan rumbunan ajiyar kayayyaki da ke kan iyakokin kasashen da suka yi makwabtaka da Najeriya.
Tilas a rika daure kayan da za a shigo da shi a cikin kwalaye ko buhuna masu ingancim saboda ba kowane irin tarkace ne Najeriya za ta sake bari a shigo ma ta da shi daga wasu kasashe ba.
Duk dan wata kasar da zai shigo Najeriya ko wani wanda zai fita daga Najeriya, tilas ya kasance ya fita ko ya shigo kan iyakokin da aka amince a shigo. Kuma ya kasance ya kai kan sa wurin jami’an kula da shigi da fice da ke kan iyakar, kuma ya kasance ya na da takardun amincewa shigowa kasar nan.
Nan da makonni biyu Najeriya za dauki nauyin zaman nazarin wannan ka’idoji tare da wakilai daga Jamhuriyar Benin, Nijar da na Najeriya.
Shugabannin Ma’aikatun Harkokin Waje, Cikin Gida, Kudade, Kwastam, Shige-da-fice, Tsaro na NIA da sauran jami’an bangarorin tsaro na kowace kasashen uku za su kasance cikin wannan kwamiti.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya ce sai ranar 31 Ga Janairu, 2020 sannan za a sake jaraba bude kan niyakokin.