Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi tayin bukatar kafa wata kakkarfar majalisa domin karfafa dankon zumuncin inganta hakokin kasuwanci da sauran huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Wannan shawara a cin mata ne a tsakanin Buhari Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman da Shugaba Buhari, a matsayin daya daga cikin manyan muhimman batutuwan da shugabannin Najeriya da Saudiyya suka dauka.
Kasashen biyu dai su na a sahun gaba na manyan kasashe masu arzikin man fetur a duniya. Saudiyya ce ta farko, sai Najeriya ta bakwai.
Da farko an shirya gudanar da taro tsakanin shugabannin kasashen biyu, a fadar Yarima Salman, amma daga baya saboda girmamawa, sai Salman ya zabi gaya ya yi tattaki ya samu Buhari har babban dakin da aka saukar da shi a shahararren otal din nan na Riyadh, Riz Charlton Hotel.
Salman da Buhari sun amince cewa za a zabi manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki days kasashen biyu su kasance mambobin majalisar.
Sannan kuma za a kafa majalisar nan da watanni biyu masu zuwa. Mambonin majalisar za su maida yankali ne wajen karfafa dangantakar inganta tattalin arziki da sauran harkokin da suka shafi fetur a tsakanin kasashen biyu.
Shugabannin kasashen biyu sun amiince za su rika ganawa say daya duk shekara domin bita da nazarin yadda karfin huldodi da harkokin junan su ke tafiya.
Sannan kuma mambonin majalisar za su rika gudanar da taro say biyu a cikin kowace shekara.
Discussion about this post