Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta rufe gidajen buredi 22 da kamfanonin yin ruwan leda 25 a garin Maiduguri jihar Barno.
Jami’in hukumar Nasiru Mato ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Maiduguri.
Wadannan gidajen buredi da kamfanonin ruwa basu aiki cikin tsafta sannan su na amfani da sanadarorin da basu da inganci. Wasu kuma basu da rajista ma kwata-kwata.
“Mun ziyarci masallatai da coci-coci domin wayar da kan mutane game da matsaloli irin haka.
Idan ba a manta ba a watan Yuli ne hukumar NAFDAC ta dakatar da aiyukkan kamfanin sarrafa ruwan leda mai suna ‘Ummi Table Water’ dake Azare a karamar hukumar Katagum jihar Bauchi.
Jami’in hukumar Abubakar Jimoh ya ce hukumar ta dakatar da wannan kamfanin ne a dalilin rashin yin rajista da ita.
Ya kuma ce hukumar ta kuma rufe kamfanin sarrafa ruwan leda mai suna ‘T-Cee Table Water’ dake nan a Azare.
Jimoh ya ce NAFDAC za ta ci gaba da aiyukkan ta tuƙuru domin tabbatar da cewa mutane na amfani da ingantattun magunguna da abinci da ake sarrafa su daga kamfanoni masu aminci a kasar nan.