Mayu da matsafa sun yi kaka-gida a Fadar Aso Rock da Majalisar Tarayya

0

Wani babban Limamin Cocin Katolika ya yi ikirarin cewa akwai dandazon mayu da matsafa a Fadar Shugaban Kasa da Majalisar Tarayya, wadanda sun fi maida hankalin su ga daukar rayukan ‘yan Najeriya.

John Olumo ya ce wadannan mayu akwai su dankam har a cikin Gidajen Gwamnati.

“Ba wai ina magana ko nufin rauhanai da bira’izai da kurwa ko kwankwaman da ake tsorata ku da labaran su a cikin dare ba.

“Wadannan ina nufin manyan shaidanun da ke cikin gwamnati a gidajen gwwmnati. Ina nufin ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, Hausawa, Igbo, Yarabawa, Kiristoci da Musulmai na cikin gwwmnati.

” Idan aka biya ka kudin yin titi, sai ka kai yin titin har ya lalace, motoci suka rika faduwa ana hadurra ana mutuwa. Idan ba maye ba ne kai, to wane ne?

“Idan aka ba ka kudin gina asibiti da zuba magunguna a asibitoci, sai ka danne kudin, jama’a suka rika mutuwa saboda rashin magunguna da yawaitar asibitoci, to kai maye ne, mai cin rayukan ‘yan Najeriya.

“Tsoffin ma’aikata sai jigata da tagayyara su ke yi, saboda ka danne musu kudin fansho. Idan kai ba maye ba ne, to wane ne kai?”

Da ya ke huduba a coci, a Abuja kwanan baya, Olumo ya ce wadannan rukunin ma’aikata da shugabanni su ne abin tsoro, ba wata kurwar da limaman coci da malamai ke tsorata jama’a da ita ba.

Ya ce ‘yan Najeriya na fama da mayu gaba da baya. Idan ba ka yi hatsari a mota ba, to dan fashi ko masu garkuwa za su tare ka. Ko Boko Haram ko rikicin makiyaya ya ritsa da kai.

“Idan ma PDP ba ta kashe ka ba, to APC za ta gama da kai. Idan ba APC ma, to akwai tarkon ‘yan sanda, su ma masu iya gamawa da kai ne.” Inji shi.

Share.

game da Author