Daga Imam Murtadha Gusau
Litinin, 25/11/2019
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
‘Yan uwa masu albarka, ina ganin kowa dai yasan dalilin da yasa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya sallami kawun sa wato Isa Sanusi, wanda aka fi sani da Isa Pilot daga fada, kuma aka tube shi daga mukamin sa. Ya sallame shi ne daga fada, sanadiyyar cin amana, yaudara, ha’inci, da yin zagon kasa ga Mai Martaba Sarki da kuma gaba dayan ita kanta Masarautar ta Kano mai albarka.

Wannan mutum, ya zabi son abun duniya maimakon kare mutuncin abun da iyayen sa da kakannin sa suka dasa na alkhairi. Ya nemi ya jefa Masarautar Kano cikin halin ni ‘ya su. Shine adalin Sarki, bayan lokutan da aka share yana hakuri da shi, ya ga cewa ba zai iya sa ido a ruguza wannan aikin alkhairi da magabatan su suka shuka ba, shine ya sallame shi don kare mutuncin wannan gida.
Sanadiyyar haka, tun wancan lokaci, wannan mutum ya hada kai da wasu shashashun ‘yan siyasa, wadanda basu san darajar wannan masarauta ba, basu san ciwon ta ba, kai basu ma san ta yaya aka samar da ita ba, wadanda in dai zasu samu kudi, to komai za su iya yi a rayuwar su, ya yarda yayi aiki tare da su, domin a fatattaka Masarautar Kano mai dimbin tarihi. Ya yarda a rusa kowa ya rasa, ba domin komai ba, sai saboda hassadar sa ga Mai Martaba Sarki. Shi yasa kwanan nan, bayan hukuncin da kotu ta yanke na ruguza wadancan “masarautu” da gwamnati ta kirkiro ba bisa ka’ida ba, kwatsam sai wannan mutum, wato Isa Sanusi (Isa Pilot), ya tattauna da wani shedani, Dan barandar ‘yan siyasa, wai shi Fa’izu Alfindiki, ta wayar tarho, suka ci mutuncin Mai Martaba Sarki da Masarautar Kano mai albarka.
Jihadin da su Shehu Dan Fodiyo suka yi, suka kafa tarihi, suka kafa wannan daula, wadda tayi naso har zuwa Kano, yau ita ce wannan mutum yake kokarin hada kai da wasu ‘yan siyasa domin su wargaza, bukatar sa ta biya, hankalin sa ya kwanta.
Bayan sun yi wannan tattaunawa da wannan shedani, ta wayar tarho, wato Alfindiki, sai shi Alfindikin ya mayar da wannan fira ta su matsayin rubutu, ya yada ta a shafin sa na Facebook, kuma yana ta murna da farin ciki, yana cewa, wai ga ma abunda kawun Mai Martaba Sarki ya fada game da wancan hukunci na kotu.
Alfindiki ya dauka cewa duniya bata san waye Isa Sanusi (Isa Pilot) ba. To ya kamata ka sani, duniya ta riga ta san waye Isa Sanusi, kuma ta san meye ya hada su da Mai Martaba Sarki. Don haka wannan shiri naku bai yi ba. Ba ku ci nasara ba, kuma wallahi asirin ku ya tonu, sai ku sake wani shirin kuma.
Haba! Isa Sanusin ma da yayi ta tsafe-tsafe da sihirce-sihirce da aikin sa na bori da ya saba yi, kuma kowa yasan shi da shi, wai domin ya kashe Mai Martaba Sarki, ko ya hada husuma tsakanin sa da gwamna, amma da yake ta Allah ba tashi ba, don Sarki alhamdulillahi, ya rike Allah, shine aka wayi gari ya kasa yin komai a kan sa. Shine da yaga cewa, ta wannan bangaren Allah ya kare Sarki, shine ya hada kai da shedanu ‘yan uwan sa, don ayi ta rubuce-rubuce, da yin bidiyo da audiyo daban-daban, ana yada wa, da nufin zubar da mutuncin Sarki da Masarautar Kano. Dukkanin su sun manta da cewa, wanda ke da Allah ya wuce makircin dukkan mai makirci.
Ga firar da suka yi da Alfindiki, na dauko maku ita, ku karanta, kuma ba tare da na canza komai daga firar ta su ba, da abun da suka rubuta. Sai ku kara yanke wa kanku hukunci cewa, wanene Isa Sanusi (Isa Pilot). Ga shi kamar haka:
“WATA SABUWA!!! KAWUN SARKIN BADALA SUNUSI LAMIDO SUNUSI, ISA BAYERO (ISA PILOT) YA BUKACI GWAMNA DA YAYI MASA MASAURATA A TARAUNI!! Lokacin da yake zantawa da Fa’izu Alfindiki ta wayar tarho: “mu yanzu bama zancen rushe Emirates bane, mu kira da muke da gwamnatin jiha da gwamna Ganduje data kara wasu masarautu ma akai muke nema, saboda mun lura ma anfara cigaba sosai da sosai, dan haka gara akara samun cigaba ma a cikin kano, yanzu kaga muna neman ayi TARAUNI ayi mata emirate, sannan TUDUN WADA, sannan SABON GARI, duk ayi musu emirate, ai kano tana da girma sosai. Toh ni acikin wadannan sababbin emirates din ma da muke kira ayi, ina so me girma gwamna yayi min sarkin TARAUNI! Ni kar a bani daraja ta biyu ma, ayi mini daraja ta uku, su wadancan sarkin tudun wada da sabon gari ayi musu daraja ta biyu biyu, ni kuma se in zama me daraja ta uku, kaga can manyan mu sune masu daraja ta daya daya, to wannan ina ganin abinda ya kamata gwamna yayi kenan. Saboda haka in an gama se a gyara doka se akara da wata dokar kuma wadda har ila yau zata kara da wadan nan. Zancen da yake cewa a bawa gwamna hakuri, eh to mun sami labari daga wata majiya me karfi inda shi lamido yana bibiya da abawa gwamna haquri, to gwamna karka yadda sau nawa yana baka hakuri? Har kwamati aka hada aka baka hakuri!! Wannan yaudara ce, so yake yi kayi lanfau suyi maka kwanton bauna. Sun yi kokari su tade ka wajen zabe Allah be yadda ba, sunyi can Allah yafi su, sunyi nan Allah ya fisu, to inka sake yanzu aka kawo maka wasu nafsina ko hadisai dan wata biyan bukatar su ta daban hmm Allah de ya sawake, kuma daman tintini na gaya maka, kan cewa duk abinda zasu gaya maka karya suke babu Allah a ransu, abinda zasu gaya maka daban, abinda yake ransu daban. Ai a fili yake tinda ake a tarihin kano ba’a taba samun sarakuna sun shiga sha’anin siyasa ba se wannan karon a kano, an maida gidan sarki ya zama APC, an maida gidan sarki ya zama PDP, duk de gasu nan jam’iyyu suna nan a gidan sarki, ba ace kuma kar mutum yayi ra’ayin sa ba, amman ra’ayi se kayi shiru kayi abinka a zuciyar ka, wannan ina ganin shine abinda za’ayi. Gwamna karfa ka yadda da wannan abinda zasu gaya ma, Allah ina gaya maka, kawai in za kayi aiki kayi aikin ka yadda ya kamata, wannan ita ce magana domin mu muna tare da kai. Kuma za muyi kira ga duk wani me son sarauta na ko ina a NIGERIA da ya temaka mana domin mu samu mu gane hanyar da za’a bi, don wannan cece-kuce mun gaji dashi wallahi!! Me girma gwamna ka temake mu yadda Allah ya temake ka.”
Ya ku ‘yan uwa, wallahi wannan fa shine abun da suka tattauna, kuma suka yada shi. Yanzu don Allah wannan za ku yarda da cewa masoyin Masarautar Kano ne? Ya hada kai da miyagu, don kawai abun duniya, a rusa gidan su, kuma aci amanar Dan uwan sa!
Wannan dai ba komai bane su wadancan miyagun ‘yan siyasa da shi wannan mutum suke kokarin yi, kamar yadda kuka sani, illa amayar da cutar hassadar da ke damun su ne. Kuma mun san meye hassada? Kuma mun san komai mutum zai iya yi sanadiyyar hassada. Don haka ma ya kamata in dan bayyana maku meye hassada, da kuma hadarin ta.
Kamar dai yadda addinin Musulunci ya karantar, kuma Malamai suka yi bayani, hassada wani mugun ciwo ne da ke nukurkusar mai yinta a cikin zuciyar sa shi kadai.
Hassada shine jin zafi, daci, ko bacin rai a yayin da kaga wani Dan uwan ka, makwabci, aboki, kai ko ma wani kawai da ka sani a duniya, ya samu daukaka, ko wace iri ce.
Kuma suka ce hassada kala uku ce (3):
1. Akwai jin kyashi, shine mutum yaji a zuciyar sa, don me wani zai fishi wani abu a rayuwa. Kudi, Mulki ko kuma Baiwa ko Mukami.
2. Shine mutum yaji shi baya son kowa ya samu wani abun alkhairi ko karuwa sai shi kadai.
3. Mutum yaji cewa idan dai shi ba zai samu abu ba to gara kar kowa ya samu. Irin su sune suke yin a fasa kowa ya rasa.
Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, kamar yadda wasu malamai kuma suka yi bayani, hassada ita ce, ‘mutum yayi burin gushewar wata ni’ima da baiwa da Allah yayi wa mai ita, ko dai ni’imar ta zam ta addini, ko ta ilimi, ko ta mukanmi, ko ta shugabanci, kai ko dai ta wani abun duniya.’
Sannan mutane sun ka su zuwa gida biyu ta bangaren hassada:
1. Akwai wanda yake burin ni’imar dan uwan shi ta gushe, ko kuma ya dube shi da ido (wato kambun baka), sai ya cutar da shi saboda kawai hassada. Kuma a Musulunci, mun san kambun baka gaskiya ne, yana kai mutum zuwa ga kabari.
2. Akwai wanda yake hassada wa mutane, yana son
ni’imar wanda yake wa hassadar ta kau (ya talauce ko ya wulakanta) ko kuma ni’imar ta dawo wajen sa, ko dukkanin su su rasa, su tashi a tutar babu. Idan hakan ta faru to shi bukatar sa ta biya.
Sannan ita hassada sharrin ta ya kai ga, takan iya sa mai yin ta ya wuce iyaka, har ta kai shi ga yin zalunci, da aikata dukkan wasu abubuwan da basu dace ba, kai har ta kai shi ga yin kisa. Misali:
1. Hassada ita ce ta sanya Kabilah ya kashe Dan uwan sa
Habilah.
Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bamu labari cewa:
“Kuma ka karanta masu labarin ‘ya ‘yan Annabi Adamu da gaskiya. A lokacin da suka bayar da baiko, sai aka karba daga dayan su, amma ba’a karba daga dayan ba.”
Wato Allah Subhanahu wa Ta’ala ya karba daga Habilah, sai bai karba daga Kabilah ba. Sai shi Kabilah yace, (Saboda hassada wa Dan uwan sa):
“Lallai ne zan kashe ka.”
Sai Habilah ya bashi amsa da cewa:
“Abin sani dai, Allah yana karba ne daga masu takawa. Lallai idan ka shimfida hannun ka zuwa gare ni domin ka kashe ni, ni
ban zama mai shimfida hannu na zuwa ga re ka, domin in kashe ka ba, lallai ni, ina tsoron Allah
Ubangijin talikai.” [Suratul Ma’idah, aya ta: 27-31]
2. Annabin Allah, Yusuf (AS), ‘yan uwan sa sunyi ikirarin kashe shi, sai suka hadu akan suna masu cewa:
“Ku kashe Yusufu, ko ku jefa shi a wata kasa, fuskar uban ku ta wofinta saboda ku, sai kuma ku kasance a bayan sa mutane salihai.” [Suratu Yusuf, aya ta: 1-10]
Duk dalilin da ya kawo wannan, shine cutar hassada. ‘Yan uwan sa ne fa na jini, amma suka dauke shi, suka jefa shi a cikin rijiya, don kawai ya mutu, su huta. Wannan kadan daga sakamakon abunda hassada ke haifar wa kenan.
Ya ku ‘yan uwa masu girma, kuyi dubo zuwa ga Iblis, ya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi wa Annabi Adamu (AS) ni’imah a cikin Aljannah, kuma Allah ya halicce shi da hannun sa, ya kuma busa masa rai, Mala’iku kuma suka yi masa sujjadar girmamawa. Sai Iblis la’ananne (Shaidan) yayi wa Annabi Adamu hassada, kuma ya daura yaki da shi, da niyyar ya zama sanadiyyar fitar da shi daga Aljannah. Iblis yabi hanyoyin da zai bi har yaci nasara, sai da Annabi Adamu ya fita daga gidan Aljannah, saboda wata hikima da Allah yake son cikawa.
Kaiton Iblis, da ya kai wannan makurar har shela yayi, yayi sanarwar yaki da Annabi Adamu (AS) da zuri’ar sa, har zuwa ranar tashin Alkiyama. Allah Subhanahu wa Ta’ala yace:
“(Iblis yace) ina rantsuwa da halakarwar da kayi mani, zan kawar da su daga bin hanyar ka madaidaiciya.” [Suratul A’araf, Aya ta: 16]
Ya ku bayin Allah, ku sani cewa, lallai ita hassada hali ne daga halayen yahudawa, kuma dabi’a ce daga cikin dabi’un su. Sun kasance suna yiwa mutane hassada gaba daya, kuma suna yi wa muminai hassada a kebe. Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bamu labari cewa:
“Mafiya yawa daga ma’bota littafi suna burin su mayar da ku kafirci, bayan imanin ku, (miye dalili?) Saboda hassada daga rayukan su.” [Suratul Baqarah, Aya ta: 109]
Allah Subhanahu wa Ta’ala ya sake cewa:
“Ko suna hassada wa mutane ne akan abinda Allah ya basu na daga falalar sa?” [Suratul Nisa’i, Aya ta: 54]
Ya ku jama’ah, ku sani, ita hassadar nan fa wuta ce, tana cin zuciyar mai yin ta, kuma ta kan sanya mai aikata ta yin komai a duniya, don ganin ya cimma burin sa. Mai hassada idan yayi hassada wa mutum, sai yayi ta bin diddigin sa, yana bibiyar labarun sa, yana bincike a kan sa, alhali mun sani, irin wannan bin diddigi da bincike akan wani, haramun ne a Musulunci.
Annabi Muhammad (SAW) yace:
“Cututtukan al’ummar da suka gabata, za su faru ga al’ummata.” Sai Sahabbai suka ce: Ya Manzon Allah mene ne cututtukan al’umar da suka gabata? Sai Annabi (SAW) yace: “…da yiwa juna hassada, har ta kai ga wuce iyaka.” [Sahihul Jami’i]
Don haka, ya kai wanda Allah ya jarraba da cutar hassada, ka sani, lallai duk ni’imar da ka gani a hannun mutane, to daga Allah Subhanahu wa Ta’ala ta ke. Allah yace:
“Babu wata ni’imah da take zuwa maku, sai daga wajen Allah.”
Allah Subhanahu wa Ta’ala shine wanda yake bawa wannan ya kuma hana wancan, kuma ya fifita wancan akan wannan da arziki. Allah yace:
“Allah shine ya fifita sashen ku akan arziki.”
Da haka nike kira da babbar murya, ya kai mai hassada! Ka sani, a yayin da kake hassada wa mutum akan wata ni’imah ko baiwa da Allah yayi masa ta dukiya ko wani matsayi ko ilimi! Ka sani wannan ni’imar ko baiwar, ba shine ya dora kansa a kanta ba, a’a, daga Allah ne. Yana bayar da ita ga wanda ya ga dama daga cikin bayin sa, sai ya kasance kenan kai mai hassada, kana yaki ne da hukuncin Allah da kaddarawar sa. Saboda haka, ina mai yi maka nasiha da kaji tsoron Allah.
Ya kai mai hassada! Kaji tsoron Allah a karan kan ka, ka kuma yi tunani kadan, kuma ka duba, idan ya kasance wanda kake yiwa hassadar yana daga cikin salihan bayin Allah, ‘yan Aljannah, to me yasa za ka yi masa hassada akan wata ni’imah ta duniya mai gushewa! Kuma zai tafi zuwa ga Aljannah, wadda fadin ta kamar fadin sammai da kassai!?
Ya kai mai hassada!!! Kaji tsoron Allah, ina mai kiran ka da kayi tunani kadan, idan ya kasance wanda kake yiwa hassadar yana daga cikin ‘yan wuta, to me yasa za ka yi masa hassada akan wannan ni’imar ta duniya mai gushewa, kuma zai tafi zuwa wuta mai zafi (Allah ya tsare mu daga gare ta)?! Amin.
Ya kai mai hassada!!!! Shin za ka yardar wa kan ka abinda kake aikatawa mutane?! Ya kai mai hassada, ya kai makiyin ni’imah, shin za ka yarda wani yayi wa ‘ya’yan ka hassada? Shin za ka yarda ayi wa dukiyar ka hassada? Shin za ka yarda wani yayi wa aikin ka da kake yi hassada? Ko za ka yarda ayi maka? Ina tsammanin amsar da za ka bayar ta gaskiya ita ce, a’a. Shin baka ji fadin Manzon Allah (SAW) ba, inda yake cewa:
“Imanin dayan ku ba zai cika ba, har sai yaso wa Dan uwan sa abinda yake so wa kan sa.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito]
‘Yan uwa, ina kiran mu da muso junan mu domin Allah! Sannan abun da zan fada ga wanda ake yiwa hassada, da mu gaba daya, shine ina rokon Allah ya tsare mu gaba daya, daga sharrin mai hassada idan yayi hassadar.
Sannan kira na da nasiha ta zuwa ga wanda ake yiwa hassada, wanda shine ma’abucin wata ni’ima ko baiwa, ta mulki ko dukiya ko ilimi ko wanin haka, ita ce:
Ya kai wanda ake yiwa hassada, idan kana so ka kasance cikin kariyar Allah a koda yaushe, to ka zamo mai tawakkali ga Allah shi kadai, ina jan hankalin ka da kada ka dogara ga wanin Allah. Allah Subhanahu wa Ta’ala yana cewa:
“Duk wanda ya mika al’amarin sa ga Allah, to zai isar masa.”
Abin nufi anan shine, Allah zai taimake shi, ya kare shi, ya kiyaye shi daga dukkan komai.
Sannan Allah Subhanahu wa Ta’ala ya sake cewa:
“Shin ba Allah bane mai isar wa bawan sa.” [Suratul Zumar]
Ya kai wanda ake yiwa hassada! Shin kana son samun kariya? To ka nemi tsarin Allah daga masu hassada, kamar yadda Allah ya umurce mu da cewa:
“Kuma (ka tsare mu) daga sharrin mai hassada yayin da yake yin hassadar.” [Suratul Falaqi, Aya ta: 5]
Kuma Manzon Allah (SAW) yace da Abdullahi Dan Abbas (RA):
“Ka kiyaye Allah, sai ya kiyaye ka, ka kiyaye Allah, sai ka same shi a gaban ka, kuma idan za ka yi roko, to ka roki Allah, kuma idan za ka nemi tsari, to ka nemi tsari daga Allah, kuma ka sani, lallai da dukkan al’ummah za su taru akan su amfanar da kai da wani abu, ba za su taba amfanar da kai da komai ba, sai da abun da Allah ya rubuta akan (zai same ka); kuma da za su hadu baki dayan su, domin su cutar da kai da wani abu, to ba za su iya cutar da kai da komai ba, sai abun da Allah ya rubuta akan ka (zai same ka). An dauke alkalummah, kuma takardu sun bushe.” [Imam Tirmizi ne ya fidda shi]
Ya kai wanda ake yiwa hassada! Shin kana son samun tsira daga sharri da makircin masu hassada? Wallahi, ina yi maka horo da yin riko da zikirorin safiya da maraice, ka kuma yawaita ambaton Allah, sai ka zama ko da yaushe cikin kariya daga sharrin miyagu, masu hassada.
Ya kai wanda ake yiwa hassada! Yi kokarin kare kan ka daga sharrin masu hassada, ta hanyar riko da addini sosai, domin riko da addini zai kare ka daga shaidanun Aljanu da shaidanun mutane, kuma zai kare ka daga sharrin dukkan mahassada.
Ya kai mugu mai cutar hassada, ya kamata kayi burin kai ma Allah ya baka irin misalin abin da ya bawa dan uwanka. Manzon Allah (SAW) yace:
“Babu hassada (wato hassada bata halatta) sai cikin abubuwa biyu:
“Mutum ne Allah ya bashi dukiya, yana ciyar da dukiyar ta hanya mai kyau, da kuma mutumin da Allah ya bashi ilimi, kuma yana aiki da shi, kuma yana kokarin karantar da al’ummah shi.” [Bukhari da Muslim]
Ya ku ‘yan uwa na masu girma, ina mai kira a gare ku, da kuyi gaggawa wajen aikata ayyuka na kwarai, domin gaggawa wajen aikata ayyuka na kwarai adon muminai ne. Idan ka ga mutum Allah ya bashi dukiya, to ka roka masa Allah ya kara masa dukiyar, kuma ya sanya albarka a dukiyar sa, sannan kuma kai ma idan kana bukata, ka roki Allah ya baka irin nasa. Idan ka ga mutum ya haddace Alkur’ani, sai ka roki Allah ya kara masa ilimi, kuma ka roki Allah yasa kai ma ka zama irin sa, idan ka ga mutum yana da ‘ya’ya sun haddace ko suna kokarin haddace Alkur’ani, ka nemi taimakon Allah yasa ‘ya’yan ka su zama irin su. Idan ka ga Allah ya bai wa wani mulki ko ni’imar shugabanci ko matsayi a cikin al’ummah, ka rokar masa Allah ya bashi ikon sauke nauyin da aka dora masa na amanar jagoranci, maimakon kayi masa hassada! Yin burin ni’imar ta gushe, wannan dabi’ar shaidan ce da kuma yahudawa, da fasikai.
Amma shi mumini, wanda ya yarda da cewa Allah shine kadai abin bautawa, kuma ya yarda cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya, kuma Annabi Muhammadu (SAW), Annabi ne kuma Manzon Allah ne, kuma yana son tsira gobe alkiyama, to ba zai yi wa kowa hassada ba. Domin yasan da cewa, wanda yake son aljannah, baya hassada wa mutane, sai dai shi yana burin ya kasance irin su.
Don haka, ya ku ‘yan uwa na, ku sani cewa, duk wadannan masu adawa da Mai Martaba Sarki, suna yi ne saboda wannan cuta ta hassada da take addabar su, ba saboda wani abu ba. Kuma In Shaa Allahu tun da dai shi Mai Martaba Sarki mun san baya nufin kowa da sharri, duk makircin su, da sharrin su, da kulle-kullen su akan su zai kare. Kuma munyi imani dari-bisa-dari, cewa, Allah zai sanya katangar karfe tsakanin sa da hassadar su.
Kuma daga karshe, ina mai bawa Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje shawara, akan ya daina biyewa wadannan tsagerun mutane masu kokarin zubar masa da kima da mutunci akan aljihun su. Sannan yayi kokarin kiyaye mutuncin sa da mutuncin kujerar da yake akai.
Sannan ina mai bashi shawara akan kar ya yarda wadannan mutanen banza su zuga shi, yaki bin umurnin kotu. Domin wallahi kin bin umarnin kotun nan na ruguza Masarautun da ya kirkiro, zai iya jawo zubar masa da mutunci, da kuma zubar da kimar kujerar sa. Sannan ya kamata Mai girma gwamna ya sani, ci gaba da mu’amala da wadannan haramtattun Masarautu tamkar yin karan tsaye ne ga tsarin doka da oda. Haka kuma kari akan laifin raini ga kotu, wanda zai jiraye shi a karshen wa’adin mulkin sa. Wannan sako ne yake turawa ga ilahirin al’ummar Jihar Kano kenan?
Idan kunne yaji, gangar jiki ya tsira!
Ina godiya ga Allah a farko da karshe.
Wannan shine abin da ya sauwaka daga gare ni. Ina rokon Allah ya kare ni da ku daga cutar hassada, ya kuma kare mu daga sharrin mahassada, amin.
Ya Allah, muna tawassali da Sunayen ka tsarkaka, Ka tausaya muna, Ka karbi tuban mu, Ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka. Kayi muna gafara, Ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin Rahmah, Muhammad (SAW). Amin.
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi. Za’a iya samun sa ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.