A dalilin kiraye-kiraye da neman karin bayani da mutanen jihar Kaduna suka rika yi game da gyaran wasu manyan Titinan gwamnatin tarayya da na jiha da suka yi matukar lalacewa a jihar Kaduna, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi karin bayani akai kamar haka:
El-Rufai ya ce dama ruwan sama ne ake jira ya yanke.
Ga titunan:
1 – Babban Titin Nnamdi Azikwe dake Kaduna. Ana jiran ruwan sama ya tsaya ne domin a fara aikin gyara titin. Kamfanin Dangote ne zai yi wannan aiki a karkashin wani tsari na yarjejeniya da Hukumar Tara Haraji ta Kasa, FIRS.
2 – Babban Titin Birni Gwari- Funtua-Dansadau. Kamfanin Dangote ne zai yi wannan aiki a karkashin wani tsari na yarjejeniya da Hukumar Tara Haraji ta Kasa, FIRS.
3 – Titin Kaduna-Legas ta Birnin Gwari wadda ya kai tsawon akalla kilomita 100. Kamfanin Dangote ne zai yi wannan aiki a karkashin wani tsari na yarjejeniya da Hukumar Tara Haraji ta Kasa, FIRS.
4 – Sannan kuma an saka Titin Kaduna-Jos a cikin kasafin kudin 2019-2020. Gwamnati zata saka ido akai sannan tuni ma har gwamnati ta fara tattaunawa da ministan Ayyuka domin ganin aiki ya kankama da zarar an saka hannu a kasafin kudin 2020.
Gwamnan jihar Kaduna ne da kansa ya fidda wannan sanarwa a shafinsa na Facebook.