Manoman Kano sun nuna damuwa kan dakatar da rabon irin tumatir daga kamfanin Dangote

0

Manoman tumatir na Jihar Kano sun bayyana cewa dakatar da raba irin tumatir din da Dangote Farm ya daina zai iya haifar da babbar barazana ga noman tumatir a wannan kakar noman rani.

Sani Danladi-Yadakwari, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Manowa, Sarrafawa da Saida Tumatir na Jihar Kano ne ya bayyana haka jiya Litinin a Kano.

Ya ce an dakatar da raba irin tumatir din bayan an bai wa manoma 500 kacal daga cikin manoma 10,000 da aka yi wa rajistar karbar lamuni na ‘CBN Anchor Borrowers’.

Manoman sun bayyana cewa irin tumatir din da Dangote Farms ya fara rabawa, akalla zai iya samar da tan 40, 60, 80 har ma zuwa 100 na tumatir a kowace hekta daya ta gona idan dai an shuka shi kuma an bi ka’idar noman sa.

“Idan ba a yi hankali ba, to makasudin raba irin tumatir din domin a bunkasa noma tumatir din da Dangote Farms zai rika yin tumatir din gwamngwani ko na leda, to zai zama tatsuniya kawai.” Inji Yadakwari.

Yadda Shirin yake

Cikin watan Oktoba ne Dangote Farms ya kaddamar da shirin raba irin tumatir dandigali, mai auki sosai, a karkashin Shirin Bada Lamuni na ‘CBN Anchor Borrowers’.
Sai dai kuma babu zato babu tsammani sai aka dakatar da shirin raba tumatir din katsahan.

Shi ya sa Danladi Yadakwari ya ce tsaiko da kuma jinkirin da aka yi wajen dakatar da rabo irin tumatir din zai kawo cikas wajen manoma kan aikin sassabe da sharar gonaki domin shirin fara noman tumatir din wata kakar mai zuwa.

“Abin da kawai mu ka samu labari shi ne akwai wani sinadari da aka hadawa da irin tumatir din, to shi ne yan kare, wai sai an bayar da odar sa daga wata kasar waje.

“Don haka mu na fatan wannan matasala za a warware wannan matsala, domin manoma su damar shuka tumatir din su. Idan bah aka kuwa, to za a yi latti sosai ma kuwa.”

Ya yi kira ga Masana’antar Dangote Processing Company da kuma Babban Babban Najeriya, CBN, su gaggauta shawo kan wannan matsala domin su ceto dimbin manoman tumatir daga shiga tarangahuma.

Babban Manajan Dangote Farms, Abdulkarim Kaita, ya tabbatar da dakatar da shirin raba irin tumatir din, amma ya jaddada cewa za a ci gaba nan ba da dadewa ba.

Ya yankewar sinadarin hada shuka irin tumatir din ne ya haifar da tsaida rabon irin.

Amma ya ce tunda an bada odar, za a ci gaba da raba irin tumatir din a karshen watan Janairu, 2020, maimakon watan Disamba da aka yi ka’ida tun da farko.

Share.

game da Author