A ranar Talata din nan ce Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta soke dokar bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakan su na jihar kudaden fansho.
Ba kudaden fansho ne kadai majalisar dokokin ta soke ba. Kakakin Yada Labarai na Majalisar Dokokin, Mustapha Jafaru, ya fitar da takardar manema labarai cewa majalisar ta kuma soke duk wasu kudaden alawus-alawus da ake bai wa tsoffin gwamnonin da mataimakan su.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kadan bayan tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari ya rubuta wa Gwamna Bello Matawalle wasikar tunatarwa cewa ya na so a biya shi kudaden fanshon sa da sauran kudaden cefane na naira milyan 10 a duk wata da ba a biya shi ba, kuma mataimakin sa shi ma ba a biya shi din ba.
A yau Talata Kakakin Yada Labarai na Gwamna Bello Matawalle, Yusuf Idris, ta tabbatar da cewa tsohon gwamna Yari ya aika wa Gwamna Matawalle wasikar neman a biya shi kudaden.
Sai dai kuma yau Talata sai Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta soke dokar biyan wadannan kudade.
Da ya ke gabatar da kudirin soke dokar a gaban Majalisa, Shugaban Masu Rinjaye, Faruk Dosara, dan PDP daga Karamar Hukumar Maradun, ya roki sauran mambobin majalisa da su amince a soke dokar biyan wannan kudade.
Dosara ya ce ba daidai ba ne a rika kwasar wadannan makudan kudade ana bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakan su, alhali kuma ga tsoffin ma’aikatan jihar da aka shafe shekaru da yawa ba a biya su hakkin kudaden su na fansho ba.
Ya ci gaba da cewa wadannan tsoffin gwamnoni da mataimakan su na karbar naira miliyan 700 cur a kowace shekara.
Daga nan sai ya ci gaba da bayanin cewa a halin da aka ciki, jihar Zamfara ba za ta iya jure biyan wadannan zunzurutun kudade ba.
Dan Majalisa Tukur Birnin-Tudu, dan PDP daga Karamar Hukumar Bakura ne ya goyi bayan kudirin, ya ce soke biyan wadannan kudade ya ma zama tilas ga gwamnatin jihar.
Bayan wannan bayani, sai Kakakin Majalisa ya sa aka sake karanta wannan kudiri, daga nan kuma aka kafa kwamiti na bai-daya.
Bayan wannan nazari kuma sai aka sake yi wa kudirin karatu na uku.
Wannan kudiri dai za su aika wa gwamna shi, daga nan shi kuma ya sa masa hannu, yadda zai zama doka nan take.
Jafaru ya shaida cewa da zaran wannan kudirin ya zama doka, to tsoffin gwamnoni da mataimakan su na jihar ba za a kara biyan su komai ba, sai fa abin da Hukumar Raba Kudade ta gindaya a rika biyan tsoffin shugabanni na tarayya ko na jihohi kadai.
Discussion about this post